Bayan kwashe watanni 9 a Dubai, Atiku ya dawo gida Najeriya

Bayan kwashe watanni 9 a Dubai, Atiku ya dawo gida Najeriya

- Bayan kwashe watanni tara a kassar Dubai, Atiku Abubakar ya sauka gida Najeriya

- Kamar yadda makusantansa suka bayyana, dawowarsa bata da alaka da siyasa ko kadan

- An gano cewa, rashe-rashen da yankin arewa ya fuskanta ne yasa ya zo ta'aziyya

Tsohon mataimakin shugaban kasa kuma tsohon dan takarar shugaban kasa a jami'iyyar PDP a zaben 2019, Atiku Abubakar, ya dawo Najeriya bayan watanni 9 da yayi a Dubai.

Atiku ya sauka a filin jirgin Nnamdi Azikwe a daren Asabar bayan barin Najeriya tun watan Fabrairun wannan shekarar.

Saboda bin dokokin cutar Covid-19, mutanen da suka je tarbarsa basu da yawa, iyalansa ne da kuma abokan arzikinsa na kusa.

Dawowar Atiku ba don matsowar bikin dan sa, Aliyu Abubakar, wanda yake rike da sarautar Turakin Adamawa bane, The Punch ta wallafa.

Wazirin Adamawa ya dawo ne saboda cigaba da harkokinsa na siyasa, bayan barin kasar na wani lokaci.

KU KARANTA: Tirkashi: Mutane sun yiwa Donald Trump ihun bama yi a lokacin da suka je jana'iza

Bayan kwashe watanni 9 a Dubai, Atiku ya dawo gida Najeriya
Bayan kwashe watanni 9 a Dubai, Atiku ya dawo gida Najeriya. Hoto daga @Thepunch
Source: Twitter

Amintattun Atiku sun tabbatar da cewa, ba zai zauna ba har sai sun samu nasara a zaben gwamnan jihar Ondo dake tafe.

Duk da majiyoyi daga iyalan Atiku sun ce, dawowar Atiku bata da wata alaka da siyasa.

Wani makusancin iyalan Atiku, wanda yace a boye sunansa, ya sanar da manema labarai cewa, Atiku ya dawo ne don yin ta'aziyya ga masarautar Zazzau saboda rasuwar sarki Alhaji Shehu Idris, sarkin Zazzau.

Tare da ta'aziyya ga Lamidon Adamawa, Dr Barkindo Mustapha, saboda rasuwar marigayiya Khadija Mustapha, wadda take matsayin kishiyar mahaifiyar sarkin, kuma mahaifiyar matar Atiku, Hajiya Rukaiya Atiku, da kuma iyalan Adamu Modibbo, wanda bai dade da rasuwa ba.

KU KARANTA: Jerin kasashe biyar a duniya da suke da saukin samun aiki

A wani labari na daban, matashi mai shekaru 23 mai suna Olamilekan Ibidokun, ya bada labarin yadda 'yan kungiyar asiri da ke yankin Ketu ta jihar Legas suka mayar da shi makaho bayan ya ki shiga kungiyar.

Kamar yadda yace, lamarin ya faru a watan Disamban 2016 yayin da suka yi wani shagalin biki a yankin Ketu ta jihar Legas, Vanguard ta wallafa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel