Adadin mutanen da yan Boko Haram suka kashe a harin da su kaiwa gwamna Zulum

Adadin mutanen da yan Boko Haram suka kashe a harin da su kaiwa gwamna Zulum

- Kwana hudu bayan kisan babban kwamandan Soji, yan Boko Haram sun kara kai mumunan hari

- Wannan shine karo na biyu da zasu nufi gwamna Babagana Umara Zulum

- Amma tuni gwamnan ya tafi ta jirgi mai saukar angulu

Akalla mutane 30 suka rasa rayukansu a harin da yan ta'addan da ake kyautata zato yan kungiyar ISWAP ne suka kaiwa tawagar jami'an gwamnatin jihar Borno yayinda suke hanyar zuwa Baga.

Majiyoyi biyu sun bayyanawa AFP ranar Asabar cewa adadin wadanda suka rasa rayukansu ya ninku daga Juma'a zuwa yau saboda an tsinci wasu gawawwaki.

Wadanda aka kashe sun hada da yan sanda goma sha biyu, Sojoji biyar, yan sa kai hudu da masu farin hula tara.

Harin ranar Juma'a ne karo na biyu da za'a kaiwa gwamnan cikin watanni biyu.

A cewar majiyoyin da ke da masaniya game da harin, sun bayyana cewa jami'an gwamnatin sun nufi Baga ne cikin shirin da gwamnatin jihar keyi na mayar da masu gudun hijra gidajensu daga Maiduguri.

Rundunar Sojoji, yan sanda, da ya sa kai suna tare da su domin tabbatar da tsaro a hanyar.

Yan Boko Haram sun bude musu wuta ne a wani muri mai suna Korochara, kimanin kilomita 2 zuwa barikin Sojojin hadaka MNJTF Baga.

Majiyar Premium Times ta bayyana cewa an kai harin ne misalin karfe 2 na rana.

Shi gwamnan Borno tuni ya tafi cikin jirgi mai saukar angulu.

Har yanzu gwamnatin jihar Borno da hukumomin tsaro basu yi tsokaci kan harin ba.

KU KARANTA: Zan marawa Bola Tinubu baya a 2023 - Buhari

Adadin mutanen da yan Boko Haram suka kashe a harin da su kaiwa gwamna Zulum
Credit: @Presidency/GovBorno
Asali: Twitter

Wannan hari na zuwa ne kwana hudu bayan kisar Kanal DC Bako da yan Boko Haram suka kashe.

A ranar Litinin ne rundunar soji ta Najeriya ta sanar da mutuwar Kanal D. C. Bako, kwamandar runduna ta 25, wanda mayakan kungiyar Boko Haram su ka kashe a jihar Borno.

Bayan Kanar Dahiru Chiroma Bako da aka kashe, Zulum ya sanar da baiwa iyalan sauran Sojoji uku da aka kashe tare da shi milyan biyu-biyu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel