Masu kwasar kananan yara daga Arewa suna siyarwa a Kudu sun gurfana a kotu

Masu kwasar kananan yara daga Arewa suna siyarwa a Kudu sun gurfana a kotu

- Wata kotun majistare da ke zama a Gombe ta gurfanar da wasu mutum uku da ake zargi da safarar kananan yara

- Rundunar 'yan sandan jihar Goben ta cafke mutum ukun bayan an kamasu da laifin satar kananan yara suna kaiwa Kudu

- Kamar yadda dan sanda mai gabatar da kara yace, tsakanin 2018 zuwa 2019, wadanda ake zargin sun sace kananan yara 13 a Gombe

Wata kotun majistare da ke zama a Gombe ta gurfanar da wasu mutum uku a gabanta a kan zarginsu da ake yi da sata tare da siyar da wasu kananan yara 13 a jihar Anambra.

Rundunar 'yan sandan jihar Gombe a ranar 7 ga watan Satumban 2020, ta damke wasu mutum hudu da take zargi da satar kananan yara a arewa suna siyar da su a Kudancin kasar nan.

Mutum ukun da ake zargi sun hada da wata Hauwa Usman mai shekaru 28 da ke zama a Tudun Wada a Gobe, Ali Bala Shaukani mai shekaru 39 da ke zama a Jalingo, jihar Taraba da wata Nkechi Nduliye da ke zama a Nkpor a karamar hukunar Idemili a jihar Anambra.

Dukkan mutum ukun an gurafanar da su a kan zarginsu da ake da aikata laifuka biyu, Daily Trust ta wallafa.

Dan sanda mai gabatar da kara, Sifeta Habibu Danjuma Juwara ya sanar da kotun cewa , wadanda ake zargin a tsakanin 2018 da 2019 sun hada baki da wata Chioma wacce har yanzu ba a kama ba, sun sace kananan yara masu shekaru biyu zuwa biyar a Gombe.

Ya ce ana zarginsu da satar yaran tare da kaiwa jihar Anambra suna siyar da su ga masu safarar yara.

Sifeta Juwara ya sanar da kotun cewa, laifin ya ci karo da tanadin sashi na 96 da 274 na Penal Code.

Amma kuma, wadanda ake zargin sun musanta aikata laifukan kamar yadda rahoton 'yan sanda ya bayyana.

Bayan musanta aikata laifukan da ake zarginsu, dan sanda mai gabatar da kara ya bukaci kotun da ta dage sauraron shari'ar har sai sun kammala bincike.

Alkalin kotun, Japhet Maida, ya dage sauraron karar zuwa ranar 29 ga watan Satumba kuma an cigaba da tsare wadanda ake zargin.

KU KARANTA: Ban taba karbar cin hanci ba a rayuwata, duk wanda ya taba bani ya fito - Magu

Masu kwasar kananan yara daga Arewa suna siyarwa a Kudu sun gurfana a kotu
Masu kwasar kananan yara daga Arewa suna siyarwa a Kudu sun gurfana a kotu. Hoto daga @Dailytrust
Source: Twitter

KU KARANTA: Fyade a Kano: 'Yan majalisa sun mika bukatar fara yi wa masu fyade dandatsa

A wani labari na daban, dan sanda mai gabatar da kara, Hyacinth Gbakor, ya sanar da kotu a ranar 12 ga watan Augusta 2020 cewa,wata Isiana Amarachi ta Oji River a jihar Enugu ta kaiwa 'yan sandan yankin 'C' a ranar 1 ga watan Augusta 2020, rahoton cewa wani ya saceta a Abuja kuma ya kaita wurin Uttah da Ada Benjamin a Makurdi.

Amarachi tace Ada tace mata zata zauna tare da ita har sai ta haihu. Ta kara da cewa Ada ta tabbatar mata da cewa, idan har na haihu za'a biyani N300,000.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel