Da duminsa: Kasar Saudiya ta amince a ci gaba da yin Umrah, ta gindaya sharudda

Da duminsa: Kasar Saudiya ta amince a ci gaba da yin Umrah, ta gindaya sharudda

- Kasar Saudiya ta amince da dawo da aikin Umrah, amma bisa sharadin bin matakai uku, domin kiyaye barkewa ko yaduwar cutar COVID-19

- Za a fara da matakin farko a ranar 4 ga watan Oktoba, sai mataki na biyu a ranar 18 ga watan Oktoba, inda mutane 6,000 da 40,000 za su rinka yin ibada a kowacce rana

- Mataki na uku zai fara a ranar 1 ga watan Nuwamba 2020, da mutane 60,000 a kowacce rana, da wannan ake shawararta jama'a su yi rejista da wuri

Hukumar gudanarwar kasar Saudiya ta sanar da cewa, za ta bi matakai, wajen janye dokar dakatar da yin Umrah a Saudi Arabia da ta sanya sakamakon barkewar annobar COVID-19.

Ministan aikin Hajj da Umrah, Mohammed Saleh Benten ya ce za su ci gaba da daukar lafiyar al'umma a kan komai, kuma ma'aikatarsa na duba matakai 3 na dawo da ibadar.

Shafin Haramain Sharifain a Twitter, ya sanar da cewa, matakin farko, za a amincewa mutane 6,000 yin ibada a kowacce rana, matakin zai fara daga ranar 4 ga watan Oktoba, 2020.

KARANTA WANNAN: Mijina yana amfani da dadironsa domin ci mun mutunci - Matar aure ta kokawa kotu

Da duminsa: Kasar Saudiya ta amince a ci gaba da yin Umrah, ta gindaya sharudda
Da duminsa: Kasar Saudiya ta amince a ci gaba da yin Umrah, ta gindaya sharudda
Asali: Twitter

A mataki na biyu, za a amince mahajjata 15,000 su yi ibada a kowacce rana, da kuma masu yin Umrah 40,000 a kowacce rana, matakin zai fara daga ranar 18 ga watan Oktoba 2020.

A mataki na uku, za a dawo da aikin Umrah ba tare da doka ba, mutane na iya zuwa daga kowacce kasa, akalla Mahajjata 20,000 da masu Umrah 60,000 a kowacce rana.

Za a fara mataki na uku daga ranar 1 ga watan Nuwamba 2020, a cewar ma'aikatar cikin gida ta aikin Hajji da Umrah.

KARANTA WANNAN: Mutuwar Sarakunan Borno guda biyu a lokaci daya ya girgiza ni - Buhari ya magantu

A ya yin bin wadannan matakai, ma'aikatar ta ce za ta tabbatar da anbi matakan lafiya domin dakile barkewa ko yaduwar annobar COVID-19.

Ma'aikatar ta kuma jaddada bukatar yin rejistar zuwa Umrah da wuri, tana mai cewa, hukumomi ko kamfanoni da ke jigilar masu ibadar su tabbatar da yin gwajin lafiya.

A halin yanzu, al'ummar kasashe 80 ne za su iya ziyartar kasar Saudiya domin yin Umrah ba tare da bukatar takarad Visa ba, kuma za a kara adadin, a cewar ma'aikatar.

A shekarar 2019, 'yan asalin kasar Saudiya 5.3m ne suka yi aikin Umrah, sai mazauna kungiyar kasashen GCC mutum 1.2m, sai 7.5m daga sauran kasashe, da 6.4 daga 'yan ci ranin Saudiya.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi jimamin mutuwar Sarakunan Borno guda biyu - Shehun Bama, Shehu Kyari Ibn Umar El-Kanemi da Sarkin Biu Mai Umar Mustapha Aliyu.

A cewarsa, mutuwar Sarakunan guda biyu a lokaci daya, duka biyu ne mai wuyar shanyewa, kuma dole 'yan Nigeria su ji radadin mutuwar Sarakunan biyu.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa daga hadimin shugaban kasar ta fuskar watsa labarai, Garba Shehu da ya rabawa manena labarai a ranar Talata.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel