Bayan cin zaben Edo: Obaseki ya aike da sako ga Tinubu, Oshiomhole da ire irensu

Bayan cin zaben Edo: Obaseki ya aike da sako ga Tinubu, Oshiomhole da ire irensu

- Gwamna Godwin Obaseki, ya ce Asiwaju Bola Tinubu, da ire irensa, barazana ne ga demokaradiyyar Nigeria

- Obaseki ya ce babu wani sashe na dokar APC da ta samar da ofishin Ja-gaban jam'iyyar na kasa, mukamin da Tinubu ke tinkaho da shi

- Idan za a iya tunawa, Tinubu ya bukaci al'ummar Edo, su juyawa Obaseki baya a ranar zabe, sai dai, INEC ta tabbatar da Obaseki a matsayin wanda ya yi nasara

Gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki, ya ce jagoran jam'iyyar APC na kasa, Asiwaju Bola Tinubu, da ire irensa, barazana ne ga demokaradiyyar Nigeria.

Obaseki ya bayyana hakan a ranar Talata a tattaunawa da shi cikin 'Shirin Safiya' na gidan talabijin din Arise TV, wata kafar watsa labarai ta jaridar THISDAY.

Da ya ke bayyana tsohon gwamnan jihar Lagos da ire irensa a matsayin 'yan wasa, Obaseki ya ce suna wasa da demokaradiyyar kasar ne, hakan kuma babbar illa ce.

KARANTA WANNAN: Babu sauran APC, abu daya ke rike da jam'iyyar - Sanata Rochas Okorocha

Bayan cin zaben Edo: Obaseki ya aike da sako ga Tinubu, Oshiomhole da ire irensu
Bayan cin zaben Edo: Obaseki ya aike da sako ga Tinubu, Oshiomhole da ire irensu
Source: Twitter

Da ya ke karin bayani kan abunda ya ke nufi da kafaffun 'yan wasan siyasa, Obaseki ya ce babu wani sashe na dokar APC da ta samar da Ja-gaban jam'iyyar na kasa, mukamin da Tinubu ke tinkaho da shi.

"Babu wani sashe a cikin dokar jam'iyyarmu da ya samar da wani mukami wai Jagoran jam'iyya," a cewarsa.

KARANTA WANNAN: Mayakan Boko Haram sun kashe kwamandan rundunar soji a harin kwanton bauna

Ya kara da cewa, "Wannan mukamin na ja-gaban APC ne ya ba shi damar harde kafafu a cikin ofishi, yana yanke shawarar wanda zai rike mukami, ko shugabanci."

"Idan har muka ci gaba da binsu a kan wannan mummunan tsarin nasu, to ba shakka za su cutar da demokaradiyyar mu," a cewar sa.

Tinubu, a cikin wani bidiyo kafin zaben gwamnan jihar Edo na ranar 19 ga watan Satumba, ya yi kira ga jama'ar Edo da su juyawa Gwamna Obaseki baya a ranar Zaben, su zabi jam'iyyar APC.

Sai dai, bayan an kada kuri'un, hukumar INEC ta tabbar da Obaseki a matsayin wanda ya lashe zaben, inda ya lallasa dan takarar APC, Osagie Ize-Iyamu, da tazarar kuri'u masu yawa.

A wani labari, Tsohon gwamna kuma Sanata mai ci a yanzu, Rochas Okorocha, ya ce girma da kimar shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ne kawai ke rike da jam'iyyar APC a halin yanzu.

Sanata Rochas, jigo a APC, ya ce komai zai iya lalacewa a jam'iyyar matukar shugabanninta basu gaggauta daukan matakan gyara ba.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel