Jan hankali: Muhimman abubuwa 5 da suka faru a ranar da aka gudanar da zaben Edo

Jan hankali: Muhimman abubuwa 5 da suka faru a ranar da aka gudanar da zaben Edo

A ranar Asabar, 19 ga watan Satumbar 2020, hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta gudanar da zaben gwamnan jihar Edo. Jam'iyyun PDP da APC ne suka fi daukar hankulan jama'a a yayin zaben.

Abubuwa da yawa sun faru a ranar da aka gudanar da zaben jihar, sai dai Legit.ng Hausa ta yi nazarin muhimman abubuwa 5 da suka faru a ranar ta Asabar.

1. Cibiyar sa ido ta kasashen Turai ta koka kan rashin bin dokokin kariya daga COVID-19

Cibiyar sa ido da bayar da tallafin zabe ta kasashen Turai (ECES), ta ce masu zabena makarantar firamare ta Ologbosere, gunduma ta 4, mai dauke da rumfunan zabe 40, ba sa bin dokar COVID-19.

Mr Wilson Manji, mataimakin kodinetan cibiyar, ya ce duk da cewa masu kada kuri'ar na sanye da makarin fuska, sai dai ba su bayar da tazara ko wanke hannuwansu ba.

2. Obaseki, Oshiomhole sun koka kan tangardar na'urar tantance masu zabe

Jim kadan bayan da Obaseki ya kada kuri'arsa a rumfar zabensa mai lamba 19, Oredo, a karamar hukumar Oredo, ya bayyana takaicinsa kan yadda ake samun tangardar na'urar 'Card reader'.

Obaseki wanda ya ce ya shafe awanni akan layi saboda tangardar na'urar, ya ce hakan ya nuna rashin tabbas akan hukumar INEC, ga uwa uba sayen kuri'u da aka yi a fadin jihar.

KARANTA WANNAN: Kidayar Kuri'u: PDP ta sha gaban APC da banbancin kuri'a fiye da dubu 50

Jan hankali: Muhimman abubuwa 5 da suka faru a ranar da aka gudanar da zaben Edo
Jan hankali: Muhimman abubuwa 5 da suka faru a ranar da aka gudanar da zaben Edo
Source: UGC

A hannu daya, tsohon shugaban jam'iyyar APC na kasa, Oshiomhole shima ya koka kan tangardar na'urar, lokacin kada kuri'arsa a rumfa mai lamba 01, gunduma ta 10, a Uzairue, Etsako ta Yamma.

Oshiomhole ya gargadi INEC da ka da ta kuskura ta sauya sakamakon zabe ta hanyar amfani da bayanan da na'urar ta shigar.

3. Jami'an tsaro, jami'an zabe da masu kada kuri'a sun yi ta kansu a garin Urhonigbe

Rahotanni sun tabbatar da cewa, rikici ya barke a garin Urhonigbe, karamar hukumar Orhionmowon, da ya tilasta jami'an tsaro, jami'an zabe da masu kada kuri'a su yi ta kansu.

KARANTA WANNAN: Sanwo-Olu ya bayar da umurnin bude gaba daya Masallatai da Majami'un Lagos

An tabbatar da cewa wasu yan bangar siyasa sun yi harbe harbe a kokarin kwatar akwatin zabe a wasu rumfunan zabe, jami'an zaben na karkashin kulawar jami'an tsaro har bayan zaben.

4. APC ta zargi PDP da wallafa sakamakon zabe na bogi

Kungiyar yakin zaben APC ta jihar ta zargi APC ta wallafa sakamakon zabe na karya, da ke nuni da cewa jam'iyyar ce ke kan gaba da APC.

APC ta ce wallafa sakamakon zaben na bogi da PDP ta yi a kafofin sada zumunta, alama ce ta cewa PDP ta karaya, ganin yadda APC ta samu kuri'u masu yawan gaske a fadin jihar.

5. PDP ta karyata zargin APC na cewar an tayar da husuma a rumfar zaben Obaseki

Jam'iyyar PDP ta karyata zargin cewa dan takararta, Obaseki, ya jagoranci yan bangar siyasa, inda suka hargitsa zabe a rumfarsa mai lamba 4, karamar hukumar Oredo.

PDP, ya yin karyata zargin, ta yi mamakin dalilin da ya sa APC ke son ganin an haddasa rikici a rumfar zaben Obaseki, yayin da Ize-Iyamu na APC ya yi zabe a rumfarsa lami lafiya.

6. Yadda sakamakon zaben jiga jigan yan siyasar ya kasance

Obaseki ya lashe zaben rumfarsa mai lamba 19, Oredo. Ya samu kuri'u 184 yayin da Ize-Iyamu ya samu kuri'u 62. Haka zalika PDP ta samu babbar nasara a rumfa ta 01, gunduma ta 002, inda Odigie-Oyegun ya kad'a kuri'arsa.

Oshiomhole ya kawo akwatinsa na gunduma ta 10, rumfa ta 001, Estako ta Yamma, inda aka kada kuri'u 1,202, yayin da PDP ba ta samu ko kuri'a daya ba.

Ize-Iyamu ya samu nasara a akwatin sa na gunduma ta 5, da kuri'u 292, inda ya lallasa Obaseki wanda ya samu kuri'u 21 kawai.

A bangaren Shu'aibu, ya kawo akwatinsa na gunduma ta 11, rumfa ta 5 a karamar hukumar Etsako ya Yamma, inda PDP ta samu kuri'u 401 yayin da APC ta samu kuri'u 148.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel