Liverpool ta sayi gogagen dan wasan tsakiya daga Bayern Munich
- Har yanzu ba a rufe kasuwar saye da sayar da 'yan wasan kwallon kafa ba duk da kungiyoyi sun fara gabzawa a gasar wasannin kasashen nahiyar Turai ta bana
- Liverpool, kungiyar Kwallon kafa ta kasar Ingila, ta sayi gogaggen dan wasan tsakiya, Thiago Alcantara, daga kungiyar Bayen Munich ta kasar Jamus
- Thiago Alcantara, dan asalin kasar Spain, ya taimakawa kungiyar Bayern Munich wajen samun nasarar lashe kofuna da dama a gasa daban-daban a kasar Jamus da nahiyar Turai
Kungiyar kwallon kafa ta Liverpool da ke kasar Ingila ta sayi gogagen dan wasan tsakiya, Thiago Alcantara, daga kungiyar Bayern Munich a kan $26m.
Thiago, dan asalin kasar 'Andolus' wacce aka fi sani da 'Spain' a yanzu, ya saka hannu a kan kwantiragi ta zama na lokaci mai tsayi a kungiyar Liverpool.
Dan wasan mai shekaru 29 a duniya ya shafe tsawon shekaru 7 tare da kungiyar Bayern Munich.
Yayin zamansa a Bayern Munich, Thiago ya taimakawa kungiyar ta lashe kofin gasar Bundesliga, kofin Jamus da kuma kofin gasar zakarun nahiyar Turai a cikin wannan shekarar.
Da ya ke sanar da komawarsa a shafin yanar gizo na kungiyar Liverpool, Thiago ya ce; "ina cikin jin dadi da farin ciki. Na dade ina jiran wannan lokaci, dole na yi murna saboda burina ya cika."
KARANTA: Nigeria ta samu babban ci gaba a kwallon duniya, ta kara sama a matakin FIFA
A ranar Asabar, 12 ga watan Satumba, aka fara kakar wasannin Premier ta wannan shekarar, tare da wasu matasan 'yan wasa, da su ka fara tashe a kakar wasannin bara.
Bayan da dan wasan Manchester United Mason Greenwood ya zamo dan wasa mai tashe a kakar bara, jaridar AFP Sport ta duba wasu 'yan wasa biyar da za su yi tashe a kakar wasan bana.
Phil Foden (Manchester City)
Ana masa kirari da dan wasa mai baiwa a kungiyar kwallon da ta lashe kofin duniya na rukunin 'yan shekaru 17 a shekaru uku da suka wuce, akwai hasashen zai tsere sa'a a kakar wasan bana.
Barin David Silva Manchester City, ya bar babban gibi a tawagar kocin kungiyar Pep Guadiola, wanda ake sa ran Foden zai cike wannan gibi.
Guardiola ya fara nuna yardarsa akan dan wasan mai shekaru 20, lokacin da ya sanya shi a wasan karshe na kakar bara tsakaninsu da Aston Villa, inda kuma ya zamo zakaran wasan, kuma ya ba kungiyar nasara kan Real Madrid a kofin zakarun nahiyar turai.
Kalvin Phillips (Leeds)
Shekaru biyu da fara taka leda, dan wasa Phillips ya farantawa kungiyar kwallon kafa ta Leeds rai, ta hanyar basu nasarar komawa kakar wasan Premier.
A shekaru biyu da suka gabata, ana kallon kamar dan wasan ba zai tabuka komai ba, amma zuwan Marcelo Bielsa a matsayin kocin Leed a 2018, ya canja tarihin dan wasan.
Bielsa ne ya fahimci cewa Phillips ya fi taka leda da kyau idan yana buga wasan gaba, mai makon wasan kato bayan kato da ya saba bugawa a baya.
Tun bayan samun wannan canji, dan wasan mai shekaru 24 ya farfado daga doguwar sumar da ya yi, har ya zamo dan wasa mai daraja a kun kungiyar kwallon kafa ta Leeds.
KARANTA: Gasar Premier: Matasan 'yan wasa biyar masu tashe da zasu taka leda a bana
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng