Matata ta yaudare ni na siya babur daga hannun kwartonta: Magidanci ya fada wa kotu

Matata ta yaudare ni na siya babur daga hannun kwartonta: Magidanci ya fada wa kotu

- Wata mata tayi ƙarar mijin ta a kotu kan cewa mugu ne kuma ya son halaka ta inda ta nemi a raba su

- Matar ta ce mijin ta ya hana ta aiki kuma baya kula da ita da yara sai duka duk lokacin da ta tambaye shi kuɗi

- A bangarensa mijin ya yi iƙirarin cewa matar da haɗa baki da kwartonta sun sayar masa babur a kan bashi

Isaac Ayodele wani tsohon ma'aikacin banki, a ranar Alhamis ya shaida wa alƙalin kotun gargajiya da ke a Mapo Ibadan cewa matarsa Omotayo ta yaudare shi ya siya babur daga hannun kwartonta.

Kamfanin Dillancin Labarai, NAN, ta ruwaito cewa Ayodele ya kuma fada wa kotu cewa matarsa tana cin amanarsa na aure.

"Na ce matata ta dena aiki bayan na samu aiki. Amma daga baya sai na rasa aiki na sai na ƙyalle ta ta fara sayar da abinci daga nan ta fara bin maza.

DUBA WANNAN: Bill Gates: Abinda Najeriya za ta yi don tsamo 'yan kasarta daga ƙangin talauci

Matata ta yaudare ni na siya babur daga hannun saurayinta: Magidanci ya fada wa kotu
Matata ta yaudare ni na siya babur daga hannun saurayinta: Magidanci ya fada wa kotu
Source: Getty Images

"Ina son sake sabuwar rayuwa sai Omotayo ta haɗa ni da kwarton ta a matsayin sai sayar da babur da zai amince in riƙa biyan kuɗin a lokaci zuwa lokaci.

"A lokacin da na gano abinda suke yi, ita da kwarton ta sun yi barazanar za su kashe ni.

"Ta kwashe kayan ta daga gida na daga baya ta kwashe yaran mu," in ji shi.

Matarsa, Omotayo a bangarenta ta ce ta shigar da ƙarar ne domin ta tsira da ranta.

A cewar ta Ayodele mutumin banza ne da ke dukan ta duk lokacin da ta nemi taimakon kudi daga hannunsa.

KU KARANTA: Hotuna: Wani mutum ya auri surukarsa bayan rabuwa da matarsa

"Miji na mugu ne kuma baya nufi na da alheri. Ya hana ni aiki ya kuma ƙi kula da ni da yara na.

"Duk lokacin da na tambaye shi kuɗi sai ya doke ni. Bayan an kore shi daga aiki mai gidan hayar mu ya tashe mu sai yaya na ya kama min gidan haya.

"Na nemo masa babur ya siya amma ya ƙi cika alƙawari. Mai babur ɗin ya kira ƴan sanda sun kama ni," in ji Omotayo.

Alƙalin kotun ya bukaci su kawo hujjoji game da zargin da suka yi wa juna ya kuma dage cigaba da sauraron shari'ar zuwa ranar 13 da watan Oktoba.

A wani labarin daban, wani dan kasuwa, Iga Bale, a ranar Laraba ya roki kotun gargajiya da ke Nyanya Abuja ta raba aurensa da matarsa Liza a kan cewa ta rantse sai ta gallaza masa ta mayar da shi tamkar mabaraci.

Bale ya roki wannan alfarman daga hannun kotu ne cikin takardar neman raba aure da ya shigar a kotun.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel