Da duminsa: Nigeria ta samu babban ci gaba a kwallon duniya, ita ce ta 29 - FIFA

Da duminsa: Nigeria ta samu babban ci gaba a kwallon duniya, ita ce ta 29 - FIFA

- Super Eagles ta haura zuwa mataki na 29 a jadawalin kungiyoyin kwallon kafa na kasashen duniya, amma har yanzu itace ta uku a kasashen Africa

- Daga kasashen Afrika, har yanzu Senegal ce a kan gaba, Tunisia ta biyu, Algeria da Morocco suna rike na hudu da na biyar

- Sai dai a jadawalin FIFA na duniya, Belgium, France, Brazil da England sune a rukunin 1 zuwa 4, yayin da Potrugal ta zakuda zuwa na 5 da ga ta 7

Kungiyar kwallon kafar Nigeria, Super Eagles ta haura zuwa mataki na 29 a jadawalin kungiyoyin kwallon kafa na kasashen duniya, amma har yanzu itace ta uku a kasashen Africa.

Bayanin hakan na kunshe ne a cikin sabon jadawalin da hukumar kula da kwallon kafa ta duniya FIFA ta wallafa a ranar Alhamis.

Babu wani canji da aka samu a jadawalin kasashen Africa, inda Senegal ta ke kan gaba, yayin da Carthage Eagles ta Tunisia ke na biyu, sai Nigeria na Uku.

KARANTA WANNAN: Shugaban kasa Buhari ya marabci shugaban kasar Burkina Faso (Hotuna)

Da duminsa: Nigeria ta samu babban ci gaba a kwallon duniya, ita ce ta 29 - FIFA
Da duminsa: Nigeria ta samu babban ci gaba a kwallon duniya, ita ce ta 29 - FIFA
Asali: Twitter

Kasar Algeria ce ta uku, sai kuma kasar Morocco a na biyar, jadawalin kungiyoyin kwallon kafa na Afrika da ya jima bai canja ba.

Haka zalika, a bagaren jadawalin na matakin duniya baki daya, kasar Belgium, France, Brazil da England sune a rukunin 1 zuwa 4, yayin da Potrugal ta zakuda zuwa na 5 da ga ta 7.

Sai dai abokan karawar Super Eagles a tankaden gasar AFCON 2021, ba su samu ci gaba ba. Ya yin da Benin Republic da Leostho suka ci gaba da zama na 84 da 139, sai Sierra Leone da ta sauko zuwa ta 119.

KARANTA WANNAN: Karin kuɗin wutar lantarki: Da sannu ƴan Nigeria za su gane amfanin hakan - FG

A daya hannun, babu wani ci gaba da Cape Verde, Central Africa Republic da Leberia suka samu. Cape Verde na a lamba ta 78, CAR ita ce ta 110, yayin da Leberia ta koma ta 152.

A wani labarin, Kylian Mbappe ya bawa kungiyar PSG da mahukuntanta mamaki bayan ya sanar dasu cewa zai bar kungiyar a karshen kakar wasannin bana.

Mbappe, dan wasan gaba a kungiyar PSG da kasar Faransa, yana shirin girgiza duniyar kwallon kafa bayan ya nuna alamun cewa zai koma kungiyar Manchester United ko Liverpool a kasar Ingila.

Ma su nazarin harkokin wasanni sun bayyana cewa manyan kungiyoyin kwallon kafa irinsu Barcelona da Real Madrid za su shiga zawarcin dan wasan duk da ya nuna cewa Ingila ya ke son komawa.

A shekarar 2018 ne kungiyar PSG ta sayi Mbappe a kan Yuro miliyan dari da hamsin da biyar (E165m) kuma har yanzu da sauran shekara biyu a kwantiraginsa.

A cewar jaridar The Times, Mbappe ya sanar da PSG cewa zai dan jinkirta barin kungiyar domin basu damar tattara kudin sauyin kungiyar da zai yi.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel