Karin kuɗin wutar lantarki: Da sannu ƴan Nigeria za su gane amfanin hakan - FG

Karin kuɗin wutar lantarki: Da sannu ƴan Nigeria za su gane amfanin hakan - FG

- Gwamnatin tarayya ta jaddada cewa nan gaba kadan yan Nigeria za su fahimci manufar gwamnati na kara kudin wutar lantarki

- Laolu Akande, hadimin mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ta fuskar watsa labarai, ya roki yan Nigeria da su ci gaba da yi wa gwamnati uziri

- A cewar sa, dukkanin wadanda suke samun wutar lantarki ta kasa da awanni 12, su sanar da gwamnati, za ta dauki mataki akai

Laolu Akande ya kare gwamnatin tarayya biyo bayan cece kuce da mamaye kasar sakamakon karin kudin wutar lantarki, yana mai cewa komai zai koma dai dai nan ba da jimawa ba.

Akande, hadimi na musamman ga mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo, ta fuskar watsa labarai, ya yi amanna da cewa karin kudin zai amfani 'yan Nigerian.

"Mutanen da muke yin yarjejeniyar da su a kwadago, suma yan Nigeria ne. Za mu tabbatar masu da hakan," a cewarsa, yayin zantawa da Channels TV, a ranar Talata.

KARANTA WANNAN: Arangama tsakanin magoya baya: Rayuwata ake nema - dan takarar PDP a Ondo

Karin kudin wutar lantarki: Da sannu 'yan Nigeria za su gane amfanin hakan - FG
Karin kudin wutar lantarki: Da sannu 'yan Nigeria za su gane amfanin hakan - FG
Asali: Twitter

"Babban abun lura a nan shine makomar kasarmu a nan gaba; tunaninmu, gaskiyarmu, rukon amana da kuma jajurcewarmu. Muna da tabbaci yan Nigeria za su fahimci hakan."

Ya yin da ya ke yin nuni da cewa kowanne dan Nigeria yana da kashi a gindinsa, Akande ya roki 'yan Nigeria da su ci gaba da yiwa gwamnati hakuri.

Akinde yana da yakinin cewa karin farashin kudin wutar lantarki, shine mafi dacewa a wannan lokaci, ma damar ana so a kawo ci gaba mai amfani a Nigeria.

"Ya kamata 'yan Nigeria su fahimci matakan kariya da shugaban kasa ya sanya masu, kuma su yi mashi uziri akan kuncin da hakan zai kawo," a cewar hadimin.

KARANTA WANNAN: Yakin neman zabe: Atiku ya mayar wa Tinubu martani a kan zaben Edo

Dangane da matakan da gwamnati ke dauka don alkinta kudaden haraji, ya jaddada cewa da yawan 'yan Nigeria za su dawo ba sa biyan kudin wutar lantarki.

A cewar sa, dukkanin wadanda suke samun wutar lantarki ta kasa da awanni 12, su sanar da gwamnati, za ta dauki mataki akai.

"Shugaban kasa ya kuma ce dole a samar da wadatattun mitocin wutar lantarki a kasar, a yanzu zamu fara kawo mitoci miliyan biyar," a cewar sa.

Kungiyar kwadago ta yi barazanar saka kafar wando daya da gwamnati akan karin kudin wutar lantarki da farashin man fetur, inda har a ranar Talata ta gana da wakilan gwamnatin tarayya.

Taron wanda Ministan kwadago Chris Ngige ya kira tare da kungiyar kwadago ta TUC da NLC a fadar shugaban kasa, Abuja, ya waiwayi dalilin karin kudaden.

A wani labarin, Sarki Auwalu, shugaban hukumar kula da cinikayyar man fetur (DPR), ya ce gwamnatin tarayya (FG) ta na da burin maye guraben motoci ma su amfani da man fetur da ma su amfani da sinadarin gas.

A cewar Auwalu, burin FG shine ganin motoci ma su amfani da sindarin gas sun zama ma fi rinjaye a Najeriya nan da wasu shekaru kadan ma su zuwa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel