PDP ta jinjinawa USA a kan hana masu magudin zaben Kogi da Bayelsa shiga kasar

PDP ta jinjinawa USA a kan hana masu magudin zaben Kogi da Bayelsa shiga kasar

- Jam'iyyar PDP ta jinjinawa haramta wa wasu 'yan Najeriya visa da Amurka tayi a kan magudin zaben da suka tafka a jihohin Kogi da Bayelsa

- PDP ta sanar da hakan ne a wata takardar da sakataren jam'iyyar na kasa, Kola Ologbondiyan ya fitar

- Kakakin jam'iyyar ya sake bukatar cewa a kara saka takunkumin hana visa a kan iyalan wadanda aka hana

Bayan saka wa wasu 'yan Najeriya takunkumin hana visa sakamakon tafka magudin zaben da suka yi, jam'iyyar PDP ta jinjinawa kasar Amurka a kan hakan.

Babbar jam'iyyar adawar a wata takarda da Kola Ologbondiyan, sakataren yada labarai na jam'iyyar ya saka hannu a ranar Talata, 15 ga watan Satumba, ya ce masu magudin zaben suna zagon kasa ga damakoradiyya.

Jam'iyyar PDP ta kara da bukatar kasar Amurka da ta kara takunkumin a kan iyalan wadanda suka tafka magudin zaben.

A yayin ci gaba da bayani, Ologbondiiyan ya bukaci da a kwace kadarorin wadannan makiyan damokaradiyyan saboda hakan ya zama izina ga sauran masu son aikata abinda suka yi

KU KARANTA: Budurwa ta rayu bayan ta fado daga bene mai hawa 8, yayin da take gujewa saurayinta

PDP ta jinjinawa USA a kan hana masu magudin zaben Kogi da Bayelsa shiga kasar
PDP ta jinjinawa USA a kan hana masu magudin zaben Kogi da Bayelsa shiga kasar. Hoto daga ThisDay
Asali: Twitter

KU KARANTA: Bidiyon wajen da aka binne marigayi Sanata Ajimobi da aka cika wajen da kayan alatu, da wutar lantarki wacce bata daukewa

Kamar yadda kakakin jam'iyyar PDP yace, matsayar kasar Amurka na bayyana cewa dukkan zabukan 2019 da aka yi da sauran zabukan da APC ta gudanar an tafka magudi.

PDP ta kara da cewa, idan har aka hana 'yan siyasa shiga sauran kasashen duniya, hakan zai zama babban jan kunne ga shugabannin APC domin su kiyaye tsaro da magudi a yayin zabe.

A wani labari na daban, gwamnatin Amurka ta ce ta saka wa wasu mutane takunkumi hana su shigar ƙasar ta saboda magudin zabe da suka yi yayin zabukkan gwamna a jihohin Kogi da Bayelsa da aka yi a 2019.

Wannan na zuwa ne a lokacin da ake shirin yin zabukkan gwamnoni a jihohin Edo da Ondo a watan Satumba da Oktoba na 2020.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel