COVID-19: Matakin da gwamnatin Saudiya ta dauka kan rufe iyakoki da sufurin jiragen sama

COVID-19: Matakin da gwamnatin Saudiya ta dauka kan rufe iyakoki da sufurin jiragen sama

- A ranar 15 ga watan Satumba 2020 gwamnatin kasar Saudiya ta shirya bude iyakokin kasar tare da amincewa da bude tashoshin jirage

- Wadanda aka amince su shiga ko fita daga kasar a yanzu sun hada da ma'aikatan gwamnati, jami'an tsaro, dalibai, marasa lafiya da sauransu

- A ranar 1 ga watan Janairu 2021 ne gwamnatin kasar ta ce za ta bude iyakokin kasar, tashohin jiragen sama da na ruwa gaba daya

Gwamnatin Saudiya ta amince da ranar 15 ga watan Satumba ta zama ranar bude iyakoki da tashoshin jiragen ruwa da na sama na kasar, amma budewar wucin gadi.

Idan za a iya tunawa, a watan Maris, gwamnatin Saudiya ta haramta tashoshin jiragen sama yin aiki domin dakile yaduwar cutar COVID-19 a kasar.

A cewar wata sanarwa a shafin masarautar kasar a Twitter a ranar Litinin, janye dokar ya shafi ma'aikatan gwamnati da jami'an tsaro kawai.

KARANTA WANNAN: Rundunar yan sanda ta fara farautar jami'inta da aka nuna yana shan shisha

COVID-19: Matakin da gwamnati Saudiya ta dauka kan rufe iyakoki da sufurin jiragen sama

COVID-19: Matakin da gwamnati Saudiya ta dauka kan rufe iyakoki da sufurin jiragen sama
Source: Twitter

Sauran da dokar ta shafa sun hada da jami'an diflomasiyya da iyalansu, marasa lafiya da ke bukatar jinya a kasashen waje, dalibai mazauna kasashen waje.

Masu shige da fice saboda bayar da tallafin jin kai, da kuma zirga zirgar ciki da waje saboda wasanni, na daga cikin rukunin wadanda dokar ta shafa.

Sai dai sanarwar ta bayyana cewa gwamnatin kasar, ta amincewa wadanda ba 'yan kasar shiga kasar ne kawai idan suna da visa, a ke a rukunin shige da fice, aiki, ibada da ziyara kawai.

KARANTA WANNAN: Gwamnatin Kaduna ta sanar da adadin talakawan da suke rayuwa a jihar

Kafin mutum ya samu damar shiga kasar, a cewar sanarwar, sai suna da shaidar da za ta nuna basu dauke da cutar COVID-19, kuma shaidar ya zamo ba ta haura awanni 48 da yin gwajin ba.

Kasar Saudiya ta kuma sanar da cewa, ranar 1 ga watan Janairu ce za ta zama ranar bude tashohin jiragen sama da na ruwa, da iyakokin kasa, a din-din-din.

A cewar sanarwar, "a ranar 1 ga watan Janairu, 2021 ne za a dage dokar hana shige da fice kwata kwata.

"Za a sanar da izinin bude iyakokin kasar da tashoshin jiragen sama da na ruwa kwanaki 30 kafin ranar 1 ga watan Janairu 2021.

"Ma'aikatar kiwon lafiya, idan akwai bukatar hakan a lokacin, na iya sanya dokoki ga matafiya a yayin shiga ko fita daga kasar, a tashohin jiragen da iyakokin kasar."

Dangane da yiyuwar bayar da izinin ci gaba da yin Umrah, sanarwar ta ce gwamnatin kasar za ta sanar da hakan nan gaba, bayan ta yi nazari akai.

A wani labarin, jaridar Charlie Hebdo a 2015, jaridar kasar Faransan, ta sake wallafa hotunan barkwancin da suka yi shekaru 5 da suka wuce, na batanci ga Annabi Muhammadu (SAW).

A 2015, jaridar wacce tayi kaurin suna wajen yin zane zanen barkwanci, ta zana siffar Annabi, lamarin da ya fusata kungiyar wasu Musulmai, har suka kai mata hari.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel