Yari makaryaci ne, ban zabawa Matawalle kwamishanoni ba - Marafa

Yari makaryaci ne, ban zabawa Matawalle kwamishanoni ba - Marafa

- Da alamun Sanata Kabiru Marafa da Abdul Aziz Yari basu shirya sulhu tsakaninsu ba

- Marafa ya yi jerin martani kan jawaban da Yari yayi a ranar Talata

- Yayinda Yari ke ganin akwai yiwuwan sulhu, amma Marafa yace da kamar wuya

Sanata Kabiru Marafa wanda ya wakilci mazabar Zamfara ta tsakiya a majalisar dattawa, a ranar Juma'a, ya karyata kalaman tsohon gwamnan jijar, AbdulAziz Yari, cewa shi ya zabawa gwamna Matawalle Sakatare da wasu kwamishanoni.

Martanin Marafa ya biyo bayan maganan da Yari yayi ranar Talata yayinda ya ziyarci hedkwatar uwar jam'iyyar dake Abuja.

A martanin da yayi yayin hira da manema labarai a Abuja ranar Juma'a, Marafa ya ce karya ne bai nada kowa cikin gwamnatin Matawalle ba.

DUBA NAN: Wasu yan iska na shirya yadda wani tsohon gwamna zai gaji Buhari - Kabiru Marafa

Yace: "Ba gaskiya bane cewa ni na zabi Sakataren gwamnati da Kwamishanoni cikin gwamnatin PDP a Zamfara."

"Hakan ya nuna irin munafurcin Yari saboda mabiyansa sun sani sarai cewa Sakataren gwamnatin jihar da kwamishanonin mambobin wata jam'iyya ne."

"Sun yi takara a zaben 2019 karkashin jam'iyyarsu, ba APC ba. Saboda haka maganan me Yari ke yi? Kawai don abokai na ne kada na bamu mukami? "

"Kawo yanzu, shugabannin kananan hukumomi 10 sanannun yaran Yari ne, tsohon mataimakinsa da kwamishanan tsaro na yanzu duka na aiki karkashin gwamnatin Matawalle. Saboda haka magana me yake yi?"

Yayin tsokaci kan shirin da gwamna Mai Mala Buni ke yi na dinke barakar jam'iyyar, Marafa yace: "Abinda na sani shine kwamitin tun yanzu tana tafka kura-kurai saboda tana sauraron irinsu Yari masu baki biyu."

KU KARANTA WANNAN: Malamin sakandare ya lalata dalibarsa mai rubuta jarabawar WAEC

Yari makaryaci ne, ban zabawa Matawalle kwamishanoni ba - Marafa

Yari makaryaci ne, ban zabawa Matawalle kwamishanoni ba - Marafa
Source: Facebook

Legit ta ruwaito muku cewa AbdulAziz Abubakar Yari, ya bayyana cewa mambobin jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar sun shirya yin sulhun gaske yanzu bayan rikicin cikin gida tsakaninsa da Sanata Kabiru Marafa.

Amma Yari yace matsalan shine wasu daga cikin mabiya Sanata Kabiru Marafa tuni sun hada kai da gwamnatin Bello Matawalle na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP).

Tsohon gwamna Abdul Aziz Yari ya bayyana hakan ne yayinda ya jagoranci tawagar mambobin jam'iyyar zuwa wajen shugaban kwamitin rikon kwaryan jam'iyyar APC, Mai Mala Buni, a Sakatariyar jam'iyyar dake Abuja.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Ku Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel