Sabon harin 'yan bindiga: Mutum 2 sun rasu, an kone gidaje masu yawa a Kaduna

Sabon harin 'yan bindiga: Mutum 2 sun rasu, an kone gidaje masu yawa a Kaduna

- A sa'o'in farko na ranar Juma'a, 11 ga watan Satumban 2020, wasu 'yan bindiga sun kutsa kauyen Manyi-Mashin da ke Zangon Kataf

- Bayan shigarsu, sun kone gidaje masu tarin yawa tare da halaka rayukan wasu dattijai biyu da kuma kwashe dukiyoyi masu yawa

- Kamar yadda SOKAPU ta bayyana, wannan watan ya kasance na zubar jini a fadin yankin Kaduna ta kudu

Wasu 'yan bindiga sun kutsa karamar hukumar Zango Kataf da ke jihar Kaduna inda suka kashe mutum biyu tare da kone gidaje masu tarin yawa.

Kungiyar jama'a mazauna kudancin Kaduna (SOKAPU), a wata takarda, ta ce, 'yan bindiga sun shiga kauyen Manyi-Mashin da sa'o'in farko na ranar Juma'a, kuma sun kashe mutum biyu tare da yin awon gaba da wasu kadarori.

Jami'ar yada labaran kungiyar, Luka Binniyat, tace mutum biyun da suka rasu sun kone kurmus a cikin gidansu. Watan Satumba ta kasance ta zubar jini ce a yankin, The Nation ta wallafa.

SOKAPU ta ce: "A sa'o'in farko na ranar Litinin, 11 ga watan Satumban 2020, 'yan bindiga sun kutsa kauyen Manyi-Mashin da ke gundumar Zamandabo a karamar hukumar Zangon Kataf.

"Ana zargin wasu Fulani makiyaya ne suka kai harin inda suka kone kusan dukkan gidajen kauyen tare da kwashe kadarori suka yi awon gaba da su.

"An kone mutum biyu a cikin gidajensu kurmus. Wadanda suka rasu sun hada da Cecilai, wata mata mai takaba mai shekaru 62 wacce ta bar yara 6 da kuma Iliya Sunday mai shekaru 56 wanda ya bar yara 8.

"Duk da cewa jami'an rundunar Operation Safe Heaven sun yi martanin gaggawa, 'yan bindigar sun gaggauta tserewa kafin isowarsu."

KU KARANTA: Wata sabuwa: Matar mataimakin gwamna na zargin Adams Oshiomhole da yi mata barazanar kisa

Sabon harin 'yan bindiga: Mutum 2 sun rasu, an kone gidaje masu yawa a Kaduna
Sabon harin 'yan bindiga: Mutum 2 sun rasu, an kone gidaje masu yawa a Kaduna. Hoto daga The Nation
Asali: Facebook

KU KARANTA: Kana taka Allah na tashi: Ango ya mutu kwanaki kadan bayan ya auri kyakkyawar amaryar shi

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Kaduna, Muhammadu Jalige, har yanzu bai yi martani a kan lamarin ba.

A wani labari na daban, wasu 'yan bindiga wadanda ba a san ko su waye ba, sun halaka manoma biyu a jihar Nasarawa.

Ana zargin makiyaya ne suka shiga kauyen Icenyam da ke yankin Kadarko Olive a karamar hukumar Keana ta jihar.

Bayanan da aka samu duk da babu yawa a kan harin sun bayyana cewa, 'yan bindigar sun samu manoman a yayin da suke gonakinsu, Vanguard ta wallafa.

Rundunar 'yan sandan jihar ta tabbatar da aukuwar lamarin. Kamar yadda kakakin rundunar, ASP Rahman Nansel ya sanar a wata tattaunawa, ya tabbatar da aukuwar lamarin.

Ya ce tuni rundunar suka tura jami'anta domin tabbatar da zaman lafiya a yankin tare da gujewa mayar da amartani.

Titus Chahur, wanda ya samu zantawa da manema labarai a garin Kadarko, ya yi kira ga gwamnatin jihar da su gaggauta kawo karshe kashe-kashen da suka yi kamari a yankin.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel