Da duminsa: Kungiyar likitoci JOHESU da Gwamnatin Tarayya sun cimma matsaya

Da duminsa: Kungiyar likitoci JOHESU da Gwamnatin Tarayya sun cimma matsaya

- Kungiyar JOHESU ta janye yajin aikin da ta ce za ta shiga ranar Lahadi, bayan cimma matsaya da gwamnatin tarayya a ranar Juma'a

- Gwamnatin tarayya ta amince da fitar da N126bn daga kudaden tallafin COVID-19 domin bunkasa asibitoci da sanya kayan aiki a cikinsu

- An dage taron zuwa ranar 15 ga watan Oktoba domin baiwa ma'aikatar kiwon lafiya damar biyan alawus alawus ga mambobin kungiyar JOHESU

Sakamakon zaman sulhu da aka yi tsakanin gwamnatin tarayya da jami'an kungiyar masu aikin lafiya JOHESU a ranar Juma'a, kungiyar ta janye yajin aikin da za ta shiga ranar Lahadi.

An umurci kungiyoin da su tuntubi mambobinsu kan yarjejeniyar da aka yi da gwamnatin tarayyar da kuma tuntubar ma'aikatar kwadago a ranar Asabar, 12 ga watan Satumba.

Takardar bayan taro ta yi nuni da cewa gwamnatin tarayya ta amince da fitar da N126bn daga kudaden tallafin COVID-19 domin bunkasa gine gine da samar da kayan aiki a asibitocin kasar.

KARANTA WANNAN: Sabon kwamishinan rundunar 'yan sandan FSARS na kasa ya kama aiki

Da duminsa: Kungiyar likitoci JOHESU da Gwamnatin Tarayya sun cimma matsaya
Da duminsa: Kungiyar likitoci JOHESU da Gwamnatin Tarayya sun cimma matsaya
Asali: Facebook

Takardar ta yi nuni da cewa matsalar sadarwa da aka samu ya sa kungiyoyin ma'aikatan lafiyar suka gaza ganin kokarin gwamnati na bunkasa bangaren kiwon lafiyar.

Taron ya samu halartar ministan kwadago da daukar aiki, Chris Ngige; ministan cikin gida kan kwadagpo, Festus Keyamo (SAN); ministan cikin gidan kan tsaro Olorunnimbe Mamora.

Sauran mahalarta taron sun hada da shugaban kungiyar JOHESU, Biobelemoye Josiah da kuma shuwagabannin kungiyar.

A yayin taron, an cimma matsaya kan cewar za a sanya kungiyoyin kiwon lafiyar a cikin ayyukan kwamitin dakile yaduwar COVID-19 na fadar shugaban kasa PTF.

KARANTA WANNAN: Shugaban kasa Buhari: Noma shi ne mafita ga matasa masu jini a jika

Bangarorin biyu sun kuma amince akan cewar akwai bukatar sanya bangaren kiwon lafiya masu zaman kansu, domin bunkasa fannin lafiyar kasar baki daya.

Maa'ikatar lafiya ta kuma bukaci mambobin JOHESU da su gabatar da sunayen mambobinsu a ranar Litinin don amfana da tallafin annobar COVID-19 da kungiyar ta yi korafi akai tun farko.

Dangane da ma'aikatan kiwon lafiya a fannin ilimi da ba su samu damar shiga cikin masu cin gajiyar tallafi, FG ta umurci JOHESU da ta gabatar da sunayen mambobin.

Ministan lafiyar ya ce zai tuntubi sauran ministoci domin magance matsalar rashin biyan tallafin sakamakon lamarin ya shafi ma'aikatar ilimi, shari'a da tsaro.

An dage taron zuwa ranar 15 ga watan Oktoba domin baiwa ma'aikatar kiwon lafiya damar aiwatar da alkawuran da ta daukarwa kungiyar ta JOHESU.

A wani labarin; Shugaba Buhari ya jaddada cewa gwamnatinsa ta dukufa wajen farfado da fannin noma don samar da wadataccen abinci da bunkasa tattalin arzikin kasa.

Shugaban kasar ya ce mayar da hankali a fannin noma zai taimaka wajen rashin dogaron kasar da fannin danyen mai, musamman wajen kasafin kudi.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel