An kama mutane biyu da suka kaiwa Hausawa hari a jihar Rivers

An kama mutane biyu da suka kaiwa Hausawa hari a jihar Rivers

- Rundunar 'yan sandan jihar Rivers ta bayar da rahoton samun nasarar kama mutane biyu da hannu a kai wa Hausawa hari a jihar Rivers

- Rundunar ta ce tuni ta mika mutane biyun ga ofishin binciken manyan laifuka na jihar

- Ta kara da cewa mutanen wannan yanki za su iya fita su cigaba da harkokinsu kamar yadda suka saba

'Yan sandan jihar Rivers sun bayyana cewa sun samu nasarar kama mutane biyu da ake zargin suna da hannu a harin da aka kai unguwar Hausawa a ranar Lahadi a karamar hukumar Oyigbo dake jihar Rivers.

Idan ba a manta ba a ranar Asabar, an samu hatsaniya tsakanin Ibo da Hausawa, inda har mutane biyu Hausawa suka mutu sakamakon wannan rikici.

An kama mutane biyu da suka kaiwa Hausawa hari a jihar Rivers
Rivers state commissioner of police Joseph Mukan - Photo Source: PUNCH
Source: Facebook

A wata sanarwa da kwamishinan 'yan sandan jihar, Joseph Mukan, ya fitar a ranar Laraba, ta bakin kakakin rundunar 'yan sandan jihar, Nnamdi Omoni, ya kara da cewa tuni an mika wadanda ake zargin zuwa ofishin binciken manyan laifuka na jihar wato (CID).

Mukan ya ce: "Kwamishinan 'yan sandan ya kira bangarorin guda biyu domin hada kan su. An binne gawarwakin Hausawa biyu da suka mutu a bisa yadda addinin Musulunci ya tanada. An samar da tsaro a yankin kuma komai ya dawo yadda ya kamata."

KU KARANTA: Za'a yiwa daliban jihar Ogun karin aji kai tsaye ba tare da sun zana jarrabawa ba idan suka koma makaranta a ranar 21 ga watan Satumba - Dapo Abiodun

Ya bawa mutanen Oyigbo tabbacin babu wata matsala kuma, inda kuma ya bukaci su je su cigaba da harkokinsu kamar yadda suka saba ba tare da tsoro ko kuma wata fargaba ba.

Legit.ng ta kawo muku rahoton yadda kungiyar CAN da shugabannin Kiristoci na jihar Kaduna suka yi watsi da gayyatar taron neman zaman lafiya da aka gayyace su a jihar.

Taron da aka yi a yau Talata, yana daga cikin yunkurin ganin sasanci a jihar Kaduna tsakanin jama'ar da suka dade suna rikici a yankin Kudancin Kaduna.

Amma kuma, taron sasancin an shirya shi ne domin halartar mutum dari kacal daga yankin.

KU KARANTA: Da duminsa: Najeriya ta tabbata cibiyar mutuwar yara masu kasa da shekaru 5 a duniya

Shugaban kungiyar kiristoci ta kasa reshen kudancin Kaduna, Bishop Simon Peters Mutum, ya ce masu ruwa da tsaki a yankin sun ji labarin za a yi taro ne a lokacin da saura sa'o'i kadan a fara, The Punch ta wallafa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel