Ku koma makaranta - Gwamnan jihar Ogun ta umurci daliban jiharsa

Ku koma makaranta - Gwamnan jihar Ogun ta umurci daliban jiharsa

Gwamnatin jihar Ogun ta sanar da ranar da dalibai zasu koma makaranta bayan watanni biyar da zama a gida sakamakon bullar cutar Korona.

Jihar Ogun na daya daga cikin jihohi uku da aka fara sanya dokar zama a gida saboda kusancinta da jihar Legas da cutar ta bulla.

Gwamnatin jihar ta bayyana cewa daliban jihar zasu koma karatu fari daga ranar 21 ga Satumba, 2020 amma ba kamar yadda aka saba ba, TVC ta ruwaito.

A sabon tsarin, daliban firamare aji 1 - 3 zasu yi karatu daga karfe 8 zuwa 11 na safe. Sannan daliban aji 4 zuwa 6 su fara karatu daga karfe 12 zuwa 3 na rana.

A bangaren makarantun sakandare, daliban ajin JSS1 zuwa JSS3 zasu yi karatu daga karfe 8 zuwa 11 na safe, sannan daliban ajin SS1 zuwa SS3 zasu yi daga karfe 12 zuwa 3 na rana.

Gwamnatin ta yi hakan ne domin rage cinkoson dalibai da tabbatar da bada tazara tsakaninsu a azuzuwa da harabar makaranta.

KU KARANTA: Yanzu yanzu: Sabbin yan Najeriya 155 sun kamu da cutar Korona

Ku koma makaranta - Gwamnan jihar Ogun ta umurci daliban jiharsa
Ku koma makaranta - Gwamnan jihar Ogun ta umurci daliban jiharsa
Asali: UGC

Ga jerin jihohi 4 da suka sanar zasu bude makarantunsu da ranakun kawo yanzu:

1. Jihar Kogi

Gwamnatin jihar Kogi a ranar Talata ta sanar da cewa dukkan makarantu mallakin gwamnatin jihar zasu koma aiki ranar 14 ga watan Satumba, 2020.

Kwamishanan ilimin jihar, Mista Wemi jones, ya ce makarantun sun hada da Firamare, Sakandare da na gaba da sakandare.

Ya sanar da hakan ne ranar Talata, 1 ga Satumba, a Lokoja yayin hira da manema labarai.

A cewar jones, gwamnatin jihar ta yanke shawarar ne bayan tattaunawa da masu ruwa da tsaki.

2. Jihar Delta

Jami'o'i a jihar Delta zasu koma bakin aiki ranar 21 ga Satumba, 2020, watanni biyar bayan rufesu domin takaita yaduwar cutar Coronavirus.

Majiyoyi daga gwamnatin jihar sun bayyana cewa an yarje da komawan dalibai makarantar ne bayan ganawar gwamnan jihar, Ifeanyi Okowa da masu ruwa da tsaki.

3. Jihar Legas

A ranar 29 ga Agusta, 2020, Gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu ya bada umurnin bude dukkan jami'o'i mallakan gwamnatin jihar daga ranar 14 ga Satumba, 2020.

Sanwo-Olu ya bayyana hakan ne a hirar da yayi da manema labarai yau Asabar, kamar yadda TheCable ta shaida.

Hakazalika ya bayyana cewa da yiwuwan za'a bude makarantun sakandaren jihar fari daga ranar 21 ga Satumba, 2020.

An rufe makarantun ne a watan Maris sakamakon bullar cutar Korona.

Jihar Legas ke kan gaba wajen yawan adadin wadanda suka kamu da cutar Korona a Najeriya.

4. Jihar Osun

Gwamnatin jihar Osun ta sanar da ranar bude makarantun jihar.

Kwamishanar ilimin jihar, Funke Egbemode, ta sanar da hakan ne ranar Litinin inda tace za'a bude ranar 21 ga Satumba, 2020.

A cewarsa, an yanke shawarar haka ne a zaman majalisar zartaswar jihar.

Ta yi kira ga masu ruwa da tsaki su tabbatar da cewa an shirya makaman bude makarantun bisa ka'idojin da ma'aikatar Ilimi ta gindaya.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel