Tirkashi: Rikici ya hado saurayi da budurwa ta dauki wuka ta caka masa yace ga garinku nan

Tirkashi: Rikici ya hado saurayi da budurwa ta dauki wuka ta caka masa yace ga garinku nan

- Budurwa ta kashe saurayinta da wuka bayan rikici ya hado su

- An bayyana cewa musu ne ya hado su, sai ya juye ya zama fada

- Rundunar 'yan sandan jihar Delta ta bayyana cewa sun kama budurwar

Rundunar 'yan sandan jihar Delta ta kama wata budurwa mai shekaru 22 da aka bayyana sunanta da Hope David, da laifin kashe masoyinta mai suna Justice Esiri, mai shekaru 24.

An ruwaito cewa lamarin ya faru da misalin karfe 1 na ranar Alhamis, 3 ga watan Satumba, a Abraka, karamar hukumar Ethiope East dake jihar.

Tirkashi: Rikici ya hado saurayi da budurwa ta dauki wuka ta caka masa yace ga garinku nan
Tirkashi: Rikici ya hado saurayi da budurwa ta dauki wuka ta caka masa yace ga garinku nan
Asali: UGC

A yadda rahotanni suka nuna, masoyan sun samu sabani, wanda daga baya yayi sanadiyyar zama fada, inda Hope ta dauki wuka ta cakawa Justice a ciki, shi kuma ya ce ga garinku nan.

An garzaya da saurayin zuwa asibiti cikin gaggawa, amma suna isa likitoci suka bayyana cewa ya mutu.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar, DSP Onome Onovwakpoyeya, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin ga jaridar The Nation, a ranar Asabar, 5 ga watan Satumba, ya ce tun sun kama mai laifin tana hannu su.

Za su gabatar da bincike a kanta kafin su mika ta gaban kotu domin gabatar da hukunci a kanta kamar yadda doka ta tanada.

KU KARANTA: An yankewa wani mutumi hukuncin kisa bayan an tsinci gawarwakin wasu mata guda biyu a cikin firjin shi

Legit.ng ta kawo muku rahoton yadda rundunar 'yan sandan jihar Anambra ta kama wata budurwa mai shekaru 25, mai suna Oyinye Chime, wacce ke dauke da ciki, da laifin cakawa saurayinta mai suna Eleyi Azubuike wuka, inda hakan yayi sanadiyyar mutuwar shi a gidanshi dake Ochiagha dake Nkpor, a cikin jihar ranar Laraba 2 ga watan Satumba.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar, Muhammed Haruna, wanda ya bayyana haka ga manema labarai, ya ce 'yan sandan sun karbi rahoton kisan, suka kuma yi gaggawar kai ziyara wajen da lamarin ya faru a ranar Laraba din.

"Bincike ya nuna cewa marigayin ya yiwa budurwar ciki, sai ya bukaci a zubar da cikin, sai taki yadda, ita ma ta bukaci ya bata kudi da za ta kula da yaron, sai shima yaki yadda. Hakan yayi sanadiyyar rikici ya barke tsakanin masoyan har yayi sanadiyyar mutuwar marigayin."

A cewar Haruna, 'yan sanda dake aiki a ofishin dake Ogidi, tare da shugabancin DPO CSP Ekuri Remigius, sun kai ziyara wajen da lamarin ya faru inda suka yi gaggawar garzayawa da marigayin asibitin Enu Mission dake Ogidi domin ceto rayuwar shi, inda a asibitin ne aka tabbatar da cewa ya mutu. Budurwa ta kashe saurayin da yayi mata ciki, bayan ta bukaci ya biyata kudi ya ki

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel