2023: Ku manta da ƙuri'un mu Idan har kuka tsayar da ɗan arewa takarar shugaban ƙasa: Igbo sun gargaɗi PDP

2023: Ku manta da ƙuri'un mu Idan har kuka tsayar da ɗan arewa takarar shugaban ƙasa: Igbo sun gargaɗi PDP

- Ƴan kabilar Igbo sun yi wa jam'iyyar PDP gargadi game da tsayar da ɗan arewa takarar shugaban ƙasa a 2023

- Matasan ƙungiyar Ohanaeze Ndigbo sun ce tun 1999 yankinsu ke zaɓen PDP kuma lokaci ya yi da za a basu damar fitar da ɗan takara

- Sun ce idan har PDP ta tsayar da ɗan arewa hakan na nufin ba ta buƙatar ƙuri'unsu kuma duk wani ɗan Igbo da ya amince ya yi takara a matsayin mataimakin shugaban ƙasa ya nesanta kansa daga yankin

Kungiyar ƙabilar Igbo ta Ohanaeze Ndigbo reshen matasa ta gargadi jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP, kada ta sake ta tsayar da ɗan arewa takarar shugaban ƙasa a 2023.

Hakan ne ƙunshe ne cikin wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun shugaban ƙungiyar, Mazi Okechukwu Isiguzoro da sakataren ta Mazi Okwu Nnabuike.

2023: Ku manta da ƙuri'un mu Idan har kuka tsayar da ɗan arewa takarar shugaban ƙasa: Igbo sun gargaɗi PDP
2023: Ku manta da ƙuri'un mu Idan har kuka tsayar da ɗan arewa takarar shugaban ƙasa: Igbo sun gargaɗi PDP
Source: UGC

DUBA WANNAN: Bidiyo: An kama wani dumu-dumu yana ƙoƙarin yin zina da matar mai gidansa

Sanarwar ta ce, "Igbo sun zaɓi jam'iyyar PDP tun shekarar 1999. Amma akwai yiwuwar an mayar da su saniyar ware. PDP na shirin barin mulki a Arewa a 2023.

"Kada PDP ta sake da raina wa ƴan kabilar Igbo wayo. Idan har PDP na tunanin Igbo za su jira har 2031 kafin a basu damar fitar da ɗan takarar shugaban ƙasa, toh hakan na nufin jam'iyyar azzaluma ce kuma ba ta buƙatar ƙuri'un ƴan Igbo.

"Matasan Igbo ba za su zauna suna kallo PDP ta tsayar da ɗan arewa ba sannan ta zo yankin su ta yi musu daɗin baki.

"Idan PDP ba ta yi amfani da hankali ba da adalci ta tsayar da ɗan arewa a 2023, ta manta da batun zuwa ƙasar Igbo domin neman ƙuri'u a zaben shugaban ƙasa.

"Kada wani ɗan siyasar Igbo ya amince da zama ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa, duk ko wanda ya amince ya karbi wannan matsayin ya yi nesa da kasar Igbo a siyasance."

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel