Yanzu-yanzu: Tsohon mai tsaron baya na Super Eagles, Ajibade Babalade ya rasu

Yanzu-yanzu: Tsohon mai tsaron baya na Super Eagles, Ajibade Babalade ya rasu

Tsohon mai tsaron baya na kungiyar Super Eagles ta Najeriya, Ajibade Babalade ya rasu a yau Juma'a a Ibadan babban birnin jihar Oyo sakamakon buguwar zuciya.

An ruwaito cewa Babajide mai shekaru 48 ya rasu ne da rana a lokacin da ake hanyar tafiya da shi asibitin koyarwa na Jami'ar Ibadan.

Tsohon mai tsaron gidan na cikin tawagar Super Eagles da suka lashe tagwulla a gasar kofin kashashen Afirka da aka yi a Senegal a shekarar 1992.

Yanzu-yanzu: Tsohon mai tsaron baya na Super Eagles, Ajibade Babalade ya rasu
Yanzu-yanzu: Tsohon mai tsaron baya na Super Eagles, Ajibade Babalade ya rasu
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Bidiyo: An kama wani dumu-dumu yana ƙoƙarin yin zina da matar mai gidansa

Ya fara wasan ƙwallon ne a Stationery Stores a Legas a 1990 kafin ya tafi 3SC ya kuma taimaka wa Oluyole Warriors suka kai wasar ƙarshe ta kofin kwararru ta CAF a 1996.

Ya buga kwallo a kungiyar kasar waje ta kasar Ivory Coast, Korea Austria da India.

A ranar 17 ga watan Oktoban shekarar 2008 aka naɗa Babajide a matsayin manajan kungiyar kwallon kafa ta Shooting Stars.

Ya rasu ya bar mata ɗaya da yara uku dukkansu suna ƙasar Amurka.

A wani labarin da Legit.ng ta wallafa, shugaban SCOAN, Fasto T.B Joshua, ya shawarci kaftin din kungiyar Barcelona, Lionel Messi, a kan tababar da ta kunno kai a tsakaninsa da mahukuntan kulob din Barca.

Messi, haziki kuma fitaccen dan wasan kwallon kafa mai shekaru 33, ya shafe kusan shekaru 20 ya na bugawa kungiyar Barcelona wasa.

Da ya ke tofa albarkacin bakinsa a kan wannan balahira a shafinsa na Twitter, TB Joshua ya bukaci Messi a kan kar ya bar kungiyar Barcelona cikin fushi da bacin rai.

Sakon TB Joshua na cewa; "Ba shawara ce mai kyau ba a ce Lionel Messi ya bar Barcelona cikin fushi da bacin rai."

"Ba zai yiwu a kulla zumunci ko wata alaka ta kirki da mutumin da aka yi rabuwar baran-baran da shi ba. Wanna ita ce shawarar da zan bawa Messi. Tarihi zai mana hukunci," kamar yadda ya wallafa.

Sai kuma gashi dai a yanzu Messi ya sanar da cewa zai cigaba da zama a kungiyar ta Barcelona saboda ya gaza cika wasu ka'idoji da ke cikin kwantiraginsa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel