Yanzu yanzu: Gwamnatin Oyo ta janye dokar hana zirga zirga, ta ce kowa ya wala

Yanzu yanzu: Gwamnatin Oyo ta janye dokar hana zirga zirga, ta ce kowa ya wala

- Kwamitin yaki da cutar COVID-19 a jihar Oyo, ta sanar da janye dokar hana zirga zirga daga karfe 10 na dare da aka kakaba a fadin jihar

- Sai dai kwamitin ya gargadi gidan rawar dare da su kauracewa cunkusa mutane a matsattsun wurare

- Kwamitin ya shawarci al'ummar jihar da su ci gaba da kuaracewa tarurruka, amfani da makarin hanci da baki, wanke hannu da sauransu

Kwamitin yaki da cutar COVID-19 a jihar Oyo, karkashin jagorancin Gwamna Seyi Makinde, ta sanar da janye dokar hana zirga zirga daga karfe 10 na dare da aka kakaba a fadin jihar.

Sanarwa daga babban sakataren watsa labarai na gwamnan, Mr Taiwo Adisa, wacce ke dauke da rahoton zaman kwamitin na ranar 31 ga Agusta, ya ce an janye dokar ne bayan dogon nazari.

Sai dai kwamitin ya gargadi gidan rawar dare da su kauracewa cunkusa mutane a matsattsun wurare, kasancewar bincike ya nuna cutar tafi yaduwa a cunkuson jama'a.

A cewar sanarwar, za a tura da takardar bayanan kariya ga mamallakan gidajen rawar dare, ta hannun cibiyar aikin gaggawa (EOC), don gargadarsu akan barin baki barkatai a gidajensu.

Sanarwar ta kuma yi nuni da cewa kwamitin ya gargadi al'ummar jihar da su ci gaba da bin dokokin yaki da yaduwar COVID-19, kasancewar har yanzu cutar ba ta tafi gaba daya ba.

KARANTA WANNAN: Sakamakon kamuwa da COVID-19: Wani babban likita a Kaduna ya mutu

Yanzu yanzu: Gwamnatin Oyo ta janye dokar hana zirga zirga, ta ce kowa ya wala
Yanzu yanzu: Gwamnatin Oyo ta janye dokar hana zirga zirga, ta ce kowa ya wala
Asali: UGC

Sanarwar ta kara da cewa Gwamna Makinde ya yanke shawarar janye dokar ne saboda rage radadi ga 'yan kasuwa, wadanda dokar ta jefa cikin mawuyacin hali na rashin sana'a.

A cewar kwamitin, duk da cewa cutar COVID-19 ta fara yin sauki a jihar, sai dai hakan ba shi zai sa a koma gefe a zauna ba, dole a ci gaba da bin matakan dakile yaduwar cutar.

Kwamitin ya shawarci al'ummar jihar da su ci gaba da kuaracewa tarurruka, amfani da makarin hanci da baki, wanke hannu da bin sauran matakan kariya.

Sanarwar ta kuma bayyana cewa Gwamna Makinde ya umurci bangaren cibiyar EOC da su ci gaba da tattara bayanai, na yadda za a kawar da cutar daga jihar gaba daya.

A jimillace, kwamitin ya yi nuni da cewa mutane 15,700 ne suka kamu da cutar ta COVID-19, inda mutane 3,118 ne ke dauke da ita, yayin da sauran suka warke, illa 37 da cutar ta yi ajalinsu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel