Za a yi juyin juya hali idan har Biden ya zama shugaban Amurka - Trump

Za a yi juyin juya hali idan har Biden ya zama shugaban Amurka - Trump

- Trump ya bayyana musibar da za ta iya faruwa idan har Joe Biden ya zama shugaban kasar Amurka

- Trump da magoya bayan jam'iyyar Republican sun caccaki Biden da jam'iyyarsa ta Democrat na gaza janye zanga zangar Antifa da Black Lives

- Trump ya ce idan har Biden ya ci zabe to za a tayar da tarzoma da juyin juya hali a Amurka

Dan takarar jam'iyyar Democrat a zaben Amurka Joe Biden mutum-mutumi ne, wanda idan aka zabe shi a Nuwamba, zai haifar da juyin juya hali a kasar, cewar shugaba Donald Trump.

"Biden ba zai iya kwantar da tarzoma ba," cewar Trump. "Za su karbe gwamnati. Su ne ke da nasara. Idan Biden ya ci zabe, su ke da nasara. Shi mutum ne mai rauni.

"Don haka za a samu tashin hankali ... Za su zo su kwace garuruwanku. Juyin juya hali ne. Kun fahimci haka. Wannan juyin juya hali ne kuma Amurukawa ba zasu laminta ba."

A cewar Trump, daukar nauyin juyin juya halin na zuwa ne daga "masu kudin da ke da mummunar manufa, amma ba zasu samu nasara ba, za su sha kasa."

KARANTA WANNAN: Jaruma Maryam AB Yola ta fita daga Kannywood, ta daina fim

Za a yi juyin juya hali idan har Biden ya zama shugaban Amurka - Trump
Za a yi juyin juya hali idan har Biden ya zama shugaban Amurka - Trump
Source: UGC

A ranar Linitin, Biden ya zargi Trump da kasa dai daita al'ummar Amurka, hasalima yana raba kawunansu ne, kuma sakonnin shi suna wuce gona da iri da tayar da tarzoma.

Martanin Biden yazo ne bayan da Trump da magoya bayan jam'iyyar Republican suka caccake shi da jam'iyyarsa ta Democrat na kaza janye zanga zangar Antifa da Black Lives.

Yan Republican sun ce Democrat a jihohin da suke da karfin iko suna kokarin yin kullalliya ne don tayar da tarzoma idan aka zo gudanar da babban zaben kasar.

An gudanar da zanga zanga mai karfi kan nuna kin jinin wariyar launin fata a Amurka bayan da 'yan sanda suka kashe wani bakin fata George Flyod a ranar 25 ga watan Mayu.

A watan August, sabuwar zanga zanga ta fara a Wisconsin da wasu yankunan Amurka bayan da 'yan sanda suka harbe Jacob Blake, bakin fata dan kasar.

Lamarin ya sanya kazamar arangama tsakanin 'yan sanda da fararen hula musamman ma bakaken fata 'yan Amurka, wadanda ke ganin ana nuna masu wariyar launin fata.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel