Da duminsa: Surukar Atiku Abubakar kuma matar marigayi Lamido Aliyu Musdafa ta rasu

Da duminsa: Surukar Atiku Abubakar kuma matar marigayi Lamido Aliyu Musdafa ta rasu

Tsohon mataimakin shugaban Nigeria, Atiku Abubakar ya sanar da rasuwar surukarsa kuma matar marigayi Lamido Aliyu Musdafa, Hajiya Khadija Aliyu Musdafa.

Hajiya Musdafa ta rasu ne a ranar Litinin, kuma mataimakin shugaban kasar ya misaltata da mace mai kirki da dattako.

Za a binne ta a ranar Talata a garin Yola, babban birnin jihar Adamawa, kamar yadda addinin Musulunci ya tanadar.

Dan takarar shugaban kasa karkashin jam'iyyar PDP a zaben 2019 ya aika da sakon ta'aziyyarsa ga iyalan Lamidon Adamawa, HRH Muhammadu Barkindo Aliyu Musdafa da kuma iyalan gidan Musdafa.

KARANTA WANNAN: Yan fashi sun kaiwa tawagar gwamnan Edo hari, ya sha dakyar

Da duminsa: Surukar Atiku Abubakar kuma matar marigayi Lamido Aliyu Musdafa ta rasu
Da duminsa: Surukar Atiku Abubakar kuma matar marigayi Lamido Aliyu Musdafa ta rasu
Asali: UGC

Ya wallafa a shafinsa cewa, "Inna lillahi wa inna ilayhi raji’un, cike da alhini nake sanar da rasuwar suruka ta kuma matar marigayi Lamido Aliyu Musdafa, Hajiya Khadija Aliyu Musdafa.

Hajiya Musdafa ta kasance mace mai kirki, mai dattako.

"A madadin iyalaina, Ina mika sakon ta'aziyya ga Lamidon Adamawa HRH Muhammadu Barkindo Aliyu Musdafa da iyalan gidan Musdafa baki daya.

"Ina mika ta'aziyya ga gwamnati da mutanen Adamawa. Za a yi jana'izarta a ranar Talata a garin Yola, ina addu'ar Allah ya gafarta mata kura kuranta ya sanya ta a Aljanna Firdausi. Ameen."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel