Dadiyata: Gwamnatin Kaduna ta yi magana a kan bacewar barden Kwankwasiyya

Dadiyata: Gwamnatin Kaduna ta yi magana a kan bacewar barden Kwankwasiyya

- Gwamnatin Kaduna ta musanta zargin cewa akwai hannunta a bacewar dan adawar gwamnati, 'Dadiyata'

- Dadiyata ya yi kaurin suna wajen sukar gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje

- Kwamishiniyar Shari'a a jihar Kaduna, Aisha Dikko, ta ce gwamnatin Kaduna bata da masaniyar inda Dadiyata ya ke

Gwamnatin jihar Kaduna ta musanta zargin cewa akwai hannunta a bacewar dan adawar gwamnati, Abubakar Idris, wanda aka fi sani da 'Dadiyata'.

Wasu 'yan ta'adda ne suka dira har gida suka sace Dadiyata, fiye da shekara guda kenan, har yanzu babu labarinsa ko halin da yake ciki.

An saceshi ne a gidansa da yake zaune tare da iyalinsa a unguwar Barnawa da ke cikin garin Kaduna.

Rundunar 'yan sanda ta sanar da cewa wasu 'yan ta'adda ne dauke da makamai suka yi awon gaba da Dadiyata yayin da ya dawo gidansa da misalin karfe 1:00 na dare.

KARANTA WANNAN: Buhari ya rantsar da kwamitin tuntuba na majalisun dokoki da tarayya

Dadiyata: Gwamnatin Kaduna ta yi magana a kan bacewar barden Kwankwasiyya
Dadiyata: Gwamnatin Kaduna ta yi magana a kan bacewar barden Kwankwasiyya
Source: Facebook

Tun bayan saceshi, har yanzu ba a ga Dadiyata ko motarsa kirar BMW da aka tafi da shi a cikinta.

A cikin wani jawabi da kwamishiniyar Shari'a a jihar Kaduna, Aisha Dikko, ta fitar ranar Litinin, gwamnatin Kaduna ta ce bata da masaniyar inda Dadiyata ya ke.

"Ma'aikatar Shari'a ta jihar Kaduna ta na mai sanar da cewa gwamnatin Kaduna ba ta da hannu ko masaniyar inda Abubakar Idris Usman (Dadiyata) ya ke tun bayan samun rahoton saceshi.

"Duk wannan abu da ake yadawa sabanin hakan sharri ne kawai domin batawa gwamnatin Kadunan suna saboda kawai a garin Kaduna aka sace shi.

"Ita gwamnatin Kaduna kotu ta ke kai duk wani mutum da take zargin ya yi mata karya, kazafi ko kage domin ya girbi abinda ya shuka," a cewarta.

Dadiyata ya yi kaurin suna wajen sukar gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje.

Kwamishiniyar Shari'ar ta kara da cewa; "gwamnati ba ta shigar da kara ko yin korafi a kan Mista Usman ba."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel