Yanzu yanzu: SERAP ta maka shugaban kasa Muhammadu Buhari a kotu

Yanzu yanzu: SERAP ta maka shugaban kasa Muhammadu Buhari a kotu

- KungiyarSERAP ta maka Shugaban Nigeria, Muhammadu Buhari a babbar kotun gwamnatin tarayya da ke Abuja

- SERAP ta shigar da karar ne saboda gazawar Buhari na bayyana sunayen mutanen da gwamnati tace ta kwato N800bn daga wajensu

- Haka zalika, kungiyar ta bukaci kotun ta tilasta Buhari ya fadi dalilin rabawa wasu tsiraru N51bn daga asusun gwamnati

Kungiyar kwatowa talaka hakkokinsu da tabbatar da adalci (SERAP) ta maka Shugaban Nigeria, Muhammadu Buhari a babbar kotun gwamnatin tarayya da ke Abuja.

SERAP ta maka shugaban kasar ne saboda gaza bayyana sunayen mutanen da gwamnati tace ta kwato N800bn daga wajensu, da kuma ayyukan da aka yi da kudaden.

Shugaban kasar a ranar 12 ga watan Yuni, 2020 ya yi jawabi mai tsayin sakin layi 78, inda ya bayyana cewa gwamnati ta kwato N800bn daga barayin kasa.

Ya sanar da cewa an yi amfani da kudaden da aka kwato wajen gudanar da ayyukan raya kasa a sassa daban daban na kasar.

A takardar karar mai lamba FHC/ABJ/CS/1064/2020 da aka shigar a ranar Juma'a a kotun, SERAP ta bukaci kotun ta umurci Shugaba Buhari ya wallafa sunayen mutane da aka kwato kudaden daga wajensu.

Haka zalika ya wallafa ranaku, da wuraren da aka yi ayyukan da har aka batar da kudaden. Haka zalika SERAP na son hukumomin yaki da rashawa su shigo cikin lamarin.

KARANTA WANNAN: Rikici ya barke a jam'iyyar PDP reshen Ekiti, jam'iyyar ta dare gida 2

Yanzu yanzu: SERAP ta maka shugaban kasa Muhammadu Buhari a kotu
Yanzu yanzu: SERAP ta maka shugaban kasa Muhammadu Buhari a kotu
Asali: UGC

A cikin takardar, SERAP ta bukaci kotun ta umurci Buhari ya tilasta hukomin yaki da rashawarar su binciki yadda aka rabawa wasu tsiraru N51bn daga asusun gwamnati a shekarar 2019.

Daga cikin wadanda ake karar akwai Abubakar Malami, Antoni Janar na kasa kuma Ministan shari'a, da Zainab Ahmed, Ministar kudi, kasafi da tsare tsaren kasa.

Karar da SERAP ta shigar ya biyo bayan 'yancin bayanai (FoI) da ta bukata a ranar 13 ga watan Yuni, 2020 ga Shugaba Buhari, tana mai cewa: "Al'umma na da 'yancin sanin bayanan.

"Yan Nigeria na hakkin sanin yadda aka kashe N800bn da aka kwato daga mahandama da kuma dalilin rabawa wasu tsiraru N51bn daga asusun gwamnati.

"Yin bayani dalla dalla kan kudaden da ake kashewa na da matukar muhimmanci ma damar ana son a samu fahimta da kara yarda tsakanin gwamnati da al'umar da take mulka."

Lauyoyi Kolawole Oluwadare da Opeyemi Owolabi, sune suka shigar da wannan kara a madadin SERAP.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel