Daga haduwa da Buhari - Ngige ya bukaci a tsige wasu Sarakuna 12

Daga haduwa da Buhari - Ngige ya bukaci a tsige wasu Sarakuna 12

Ministan kwadago da daukar aiki, Dr Chris Ngige, ya bukaci gwamnan jihar Anambra, Willie Obiano, da ya tsige Sarakuna 12 da suka ce Abuja ganin shugaba Buhari ba tare da amincewar gwamnatin jihar ba.

A cewar Dr Chris Ngige, Prince Arthur Eze, wanda ya jagoranci tawagar zuwa Abuja, ya kamata ya fuskanci hukunci mai tsanani na wannan dan waken zagayen.

Idan ba a manta ba mun ruwaito maku cewa Gwamna Obiano ya dakatar da Sarakuna 12 saboda saboda ziyarar da suka kaiwa shugaban kasa Muhammadu Buhari a Abuja.

Gwamnatin jihar na kallon wannan ziyara a matsayin barazana da kuma karya dokokin mataki mataki na mulki, musamman da suka kebantu da masarautun jihar.

Sai dai Ngige, a wayar tarho da manema labarai a ranar Asabar, ya ce ba dakatarwa ya kamata ayiwa Sarakunan ba, kawai a tsige su shine mafi dacewa.

KARANTA WANNAN: Rundunar 'yan sanda ta yi babban rashin jami'inta a Katsina

Daga haduwa da Buhari - Ngige ya bukaci a dakatar da wasu Sarakuna 12
Daga haduwa da Buhari - Ngige ya bukaci a dakatar da wasu Sarakuna 12
Asali: UGC

Ya ce, "Idan har aka dakatar da mutum daga gudanar da ayyukan ofishinsa, to ya kamata a tsige shine kwata kwata, a koreshi daga wannan aikin.

"Barinsa yana rabar wajen ma wata fitinar ce. Domin kaucewa wannan fitinar, to kawai a koresa daga wannan wajen, don gudun barazana da karya wasu dokokin.

"Don haka, ina shawartar gwamnatin jihar Anambra, da ta kori wadannan Sarakuna 12 daga masarautunsu don gudun tayar da zaune tsaye.

"Shi dan kasuwar da ya kai Sarakunan Abuja (Arthur Eze), ya kamata na shi hukunci ya fi na kowa, don ya zama darasi ga masu tunanin yin hakan a nan gaba."

Sai dai, mai magana da yawun Mr Eze, da ya bukaci a sakaya sunansa, ya bayyana wannan kira na Ngige a matsayin karya dokar kasa da kuma son nuna karfin iko akan gwamnan jihar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel