Yanzu-yanzu: Buhari ya sallami Charles Dokubo, ya nada sabon shugaban shirin Jin-kai

Yanzu-yanzu: Buhari ya sallami Charles Dokubo, ya nada sabon shugaban shirin Jin-kai

Biyo bayan zarge zargen da ake yi masa, shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Alhamis ya kori Charles Dokubo, tare da maye gurbinsa da Milland Dikio a matsayin shugaban shirin jin kai mai taken 'Amnesty Programme' a turance.

Da ya ke sanar da hakan, Garba Shehu, ya ce: "Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da nada Kanal Millan Dixion Dikio (rtd) a matsayin sabon shugaban shirin 'Amnesty Programme'.

"Wannan ya biyo bayan amincewar shugaban kasar na sallamar Farfesa Charles Quarker Dokubo daga ofishin shugabancin hukumar, cikin gaggawa.

"An umrci Farfesa Dokubo da ya mika dukkanin takardun ofishinsa ga babban jami'in shirin.

"Haka zalika shugaba Buhari ya godewa Farfesa Dokubo akan ayyukan da ya yi."

KARANTA WANNAN: FG ta amince a biya ma'aikatan N-Power da aka sallama kudadensu

Yanzu-yanzu: Buhari ya sallami Charles Dokubo, ya nada sabon shugaban shirin Jin-kai
Yanzu-yanzu: Buhari ya sallami Charles Dokubo, ya nada sabon shugaban shirin Jin-kai
Asali: Facebook

Ma'aiakatar jin kai da bunkasa rayuwa, karkashin Sadiya Umar Farouq ta amince da a biya ma'aikatan N-Power da aka sallama kudadensu, karkashin N-SIP.

A ranar Litinin 24 ga watan Agusta 2020, Ministar ta amince da abiya basussukan da tsofaffin ma'aikatan ke bi, wadanda ke a rukuni na A da B.

Tuni dai aka tura bukatar biyan basussukan har zuwa watan Yuni, 2020 ga ofishin babban akanta na kasa domin kammala bincike da biyan kudaden.

A yanzu dai kudaden watan Yuli na wasu daga cikin 'yan rukunin B ne ba a kai ga biya ba, kuma bukatar na gaban ofishin akantan.

Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa daga hadimin ministar ta fuskar watsa labarai, Nneka Ikem Anibeze da aka rabawa manema labarai a ranar Alhamis.

Sanarwar ta bayyana cewa masu cin gajiyar shirin 14000 da aka cire sunayensu daga ofishin AGF a yayin biyan kudin watan Maris zuwa Yuni 2020, na daga cikin wadanda manhajar GIPMIS ta ki karbar bayanan bankunan biyan kudinsu.

A cewar rahoton ofishin AGF, duk wani mai cin gajiyar shirin da ke karbar albashi daga gwamnati ba zai samu kudinsa ba.

Ma'aikatar FMHADMSD ta bukaci wadanda abun ya shada da su gabatar da dalilan da ya sanya basu samu kudinsu ba daga ofishin AGF, inda ta sha alwashin yin mai yiyuwa wajen biyansu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel