Ya dawo daga banki, 'yan fashi sun kashe shi sunyi awon gaba da kudin

Ya dawo daga banki, 'yan fashi sun kashe shi sunyi awon gaba da kudin

- Wasu da ake kyautata zaton 'yan fashi ne sun kashe wani mutumi tare da awon gaba da kudinsa bayan fitowarsa daga banki

- Mutumin mai suna Taoreed Alao, ya gamu da ajalinsa ne a kan titin sakatariya da ke Agodi, Ibadan, babban birnin jihar Oyo

- Jami'in hulda da rundunar 'yan sanda na jihar Oyo, Olugbenga Fadeyi, ya tabbatar da faruwar kisan

Rundunar 'yan sanda a ranar Talata ta ce 'yan fashi sun kashe wani mutumi a ranar Litinin kusa da gidan gwamnatin jihar da ke Ibadan, bayan fitowa daga banki.

Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa mutumin mai suna Taoreed Alao, ya gamu da ajalinsa ne a kan titin sakatariya da ke Agodi, Ibadan, babban birnin jihar Oyo.

An kashe shi ne da misalin karfe 1:30 na rana bayan da 'yan fashin suka bibiyeshi tun daga bankin da yafito, suka tsayar da shi tare da harbeshi a kan mashin dinsa.

Rahotanni sun bayyana cewa mamacin ya cire N150,000 da kuma N296,000 daga wani banki a yankin Bodija, birnin Ibadan.

KARANTA WANNAN: Gwamnatin tarayya ta ciyo bashin ton 5,000 na hatsi don ciyar da 'yan Nigeria

Ya dawo daga banki, 'yan fashi sun kashe shi sunyi awon gaba da kudin
Ya dawo daga banki, 'yan fashi sun kashe shi sunyi awon gaba da kudin
Asali: UGC

Jami'in hulda da rundunar 'yan sanda na jihar, Olugbenga Fadeyi, wanda ya tabbatar da faruwar kisan ya ce, an garzaya da Mr Alao asibitin jihar Adeoyo, inda a nan ya bar duniyar.

Ya kara da cewa an ajiye gawar mamacin a cikin asibitin.

"Da misalin karfe 11:45 na safiya, a kusa da wani ginin gwamnatin jihar Oyo, wasu da ake zargin 'yan fashi ne suka harbe Taoreed Alao, mai shekaru 45.

"Sun yi awon gaba da mashin dinsa kirar Bajaj, yayin da aka hanzarta kaishi asibitin gwamnatin jihar da ke Adeoyo, inda a nan yace ga garinku nan.

"An samu gawarsa da wayoyi guda biyu, da kuma tsabar kudi N90,000. An ajiye gawarsa a asibitin a kokarin da ake na gano 'yan uwansa," a cewar jami'in hulda da jama'ar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel