Buhari ya saki biliyan N14.92 domin biyan ma'aikatan da suka yi ritaya hakkokinsu

Buhari ya saki biliyan N14.92 domin biyan ma'aikatan da suka yi ritaya hakkokinsu

Gwamnatin tarayya, a karkashin tsarin fansho na karo-karo, ta saki biliyan N14.92 domin biyan basukan hakkokin ma'aikatan da suka yi ritaya.

Hukumar kula da harkokin fansho ta kasa ce ta sanar da hakan ranar Litinin a cikin wata takarda da ta fitar.

Takardar ta bayyana cewa; "za a yi amfani da wadannan kudade domin biyan ariyas na watanni hudu."

"Wanna hukuma tana mai yabawa gwamnatin tarayya a kokarinta na ganin cewa ta biya dukkan basukan hakkokin ma'aikatan da suka yi ritaya, sannan muna godiya ga ma'aikatan da abin ya shafa saboda hakuri da juriyar da suka nuna," a cewar sanarwar.

Wannan labari na zuwa ne a daidai lokacin da rahoton hukumar kididdiga ta kasa (NBS) a ranar Litinin na nuni da cewa tattalin arzikin Nigeria na cikin gida (GDP) ya karye da kashi –6.10.

Rahoton kididdigar GDP na watanni shida na shekarar 2020 ya nuna cewa tattalin arzikin ya karye ne saboda matsalolin tattalin arziki na cikin gida da wajen kasar da aka samu.

Buhari ya saki biliyan N14.92 domin biyan ma'aikatan da suka yi ritaya hakkokinsu
Buhari
Asali: Twitter

Sai dai rahoton ya yi nuni da cewa an fi samun koma baya daga watan Afrelu zuwa Yulin 2020.

Kasashen duniya sun kulle duk wata kafar tattalin arziki sakamakon barkewar annobar COVID-19.

DUBA WANNAN: Takarar shugaban kasa 2023: Tambuwal ya nemi shawarar Obasanjo, Mark da Danjuma

A watan Maris ne Nigeria ta sanar da rufe iyakokin kasar a yunkurinta na dakile yaduwar cutar ta COVID-19 a fadin kasar.

Hukumar NBS a ranar Litinin ta yi nuni da cewa dalilan karyewar tattalin arzikin kasar sun hada da sanya dokar ta baci ga mutane da ababen hawa a jihohin kasar.

Sauran sun hada da haramta tafiye tafiye ta jiragen sama, rufe makarantu da kasuwanni da dai sauran, wanda ya shafi kasuwancin cikin gida dana waje.

Wannan hukunci da gwamatin tarayya da na jihohi suka dauka, ya kawo koma baya sosai a watanni shidan farko na shekarar, kuma da yiyuwar ya wuce hakan.

Karyewar tattalin arzikin ya zo ne bayan shekaru uku na karancin tattali amma dai wanda ba za ace ya karye ba, tun bayan karyewarsa a 2016.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel