Da duminsa: APC ta lashe kujerun kananan hukumomi 18 a jihar Ondo

Da duminsa: APC ta lashe kujerun kananan hukumomi 18 a jihar Ondo

- Jam'iyyar APC ta lashe kujerun kananan hukumomi 18 a fadin jihar Ondo

- Daga cikin 18 da aka saki sakamakonsu, kananan hukumi biyar babu abokan hamayya a zabensu, APC ce kawai ta yi zabe

- INEC ta ce an sanar da nasarar 'yan takarar ne akan tsarin dokokin hukumar zaben jihar

Jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ta lashe kujerun kananan hukumomi 18 a fadin jihar Ondo, a babban zaben jihar da aka gudanar ranar Asabar.

Shugaban hukumar INEC reshen jihar, Farfesa Yomi Dinakin, ya sanar da sakamakon zaben bayan da jami'an tattara kuri'u suka karanto adadin kuri'un kowacce karamar hukuma.

Kananan hukumomin da sakamakon zabensu yazo a sahun karshe sune Akoko ta Arewa maso Yamma, Akoko ta Kudu maso Yamma, Idanre da kuma Ondo ta Gabas.

Daga cikin 18 da aka saki sakamakonsu, kananan hukumomi biyar babu abokan hamayya a zabensu, APC ce kawai ta yi zabe.

KARANTA WANNAN: Rundunar 'yan sanda ta cafke masu garkuwa da mutane 45 da suka addabi Borno

Da duminsa: APC ta lashe kujerun kananan hukumomi 18 a jihar Ondo
Da duminsa: APC ta lashe kujerun kananan hukumomi 18 a jihar Ondo
Asali: Twitter

Shugaban hukumar zaben ya ce 'yan takarar jam'iyyar APC sun lashe zaben ba tare da hamayya ba, saboda APC ce kawai ta yi zaben kananan hukumomin.

Dinakin ya ce an sanar da nasarar 'yan takarar ne akan tsarin dokokin hukumar zaben jihar ODIEC.

Kananan hukumomin da abun ya shafa sun hada da Akoko ta Arewa maso Gabas, Ose, Ifedore, Odigbo da kuma Irele.

Zaben kananan hukumomin an gudanar da shi ne a ranar Asabar ba tare da hamayyar sauran jam'iyyun adawa ba, kamar jam'iyyar PDP.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel