Ka sallami Magu kuma ka hukuntashi - Kwamitin binciken da Buhari ya nada ta bashi shawara

Ka sallami Magu kuma ka hukuntashi - Kwamitin binciken da Buhari ya nada ta bashi shawara

Kwamitin fadar shugaban kasa da aka nada domin binciken dakataccen shugaban hukumar hana almundahana EFCC, Ibrahim Magu, ta bada shawara a sallami Magu.

A labarin da The Cable ta samu, kwamitin karkashin jagorancin tsohon Alkalin kotun afil, Ayo Isah Salami, ta baiwa Buhari jerin shawarin da tayi kuma daga ciki shine a hukunta Magu kan zargin rashawa da ci da kujerarsa.

An zargi Magu da saba dokar CCB ta hanyar kin bayyana wasu dukiyoyin da ya mallaka lokacin da ya shiga ofis a 2015.

Hakazalika, kwamitin ta baiwa Buhari shawaran cewa ya nada sabon shugaban EFCC ba tare da bata lokaci ba.

Hakan na bisa umurnin da shugaba Buhari ya yiwa mambobin kwamitin ranar 3 ga Yuli, 2020 cewa su "rika bashi rahoto lokaci bayan lokaci."

Ka sallami Magu kuma ka hukuntashi - Kwamitin binciken da Buhari ya nada ta bashi shawara
Ka sallami Magu kuma ka hukuntashi - Kwamitin binciken da Buhari ya nada ta bashi shawara
Asali: UGC

Tsohon diraktan ayyuka a EFCC, Mohammed Umar, ke jan ragamar lamura a hukumar tun ranar 6 ga Yuli bayan dakatad da Magu.

An dakatad da Magu daga ofishinsa ne ranar 7 ga Yuli, 2020 bayan zarginsa da ake yi.

An tsareshi a ofishin FCID na yan sanda dake unguwar Arewa 10, birnin tarayya Abuja kafin ya samu ne bayan kwanaki 9 a tsare.

Magu ya shiga tsaka mai wuya ne bayan takardar tuhumar da ministan shari'a, Abubakar Malami, ya rubuta kansa na laifinsa rashawa.

Ga jerin tuhume-tuhume 10 cikin 22 da ake yiwa Ibrahim Magu

1. Tufka da warwara wajen lissafin kudaden da EFCC ta kwato hannun barayin gwamnati

2. Ikirarin cewa N539bn aka kwato maimakon N504bn

3. Rashin biyayya ga ofishin Antoni Janar na tarayya

4. Rashin gabatar da isassun hujjoji domin dawo da Diezani Alison-Madueke Najeriya

5. Bata lokaci wajen binciken kamfanin P&ID wanda ahakan ya kai ga rikicin da ake a Kotu yanzu

6. Kin bin umurnin kotu na sakin asusun wani tsohon diraktan banki kimanin N7bn

7. Bata lokaci wajen daukan mataki kan jiragen ruwa biyu da hukumar Sojin ruwa ta kwace

8. Fifita wasu jami'an EFCC kan wasu wadanda akafi sani da 'Magu Boys'

9. Kai wasu Alkalai kara wajen shugabanninsu ba tare da sanar da Antoni Janar ba

10. Sayar da dukiyoyin sata ga yan'wansa, abokan arziki da abokan aiki

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel