Kano: Matashi ya sha alwashin kashe kansa ranar auren Hanan Buhari

Kano: Matashi ya sha alwashin kashe kansa ranar auren Hanan Buhari

- A yayin da ake shirin bikin diyar shugaban kasa Muhammadu Buhari, Hanan Buhari, manema aurenta sun shiga rudani

- Kamar yadda rahotanni daga jihar Kano ke nunawa, wani matashi ya yanke jiki ya fadi kuma yana kwance a gadon asibiti a halin yanzu

- Kwamared Abba Ahmed, dalibi ne da ke shekarar karshe a jami'ar North West kuma dan kasuwa ne wanda ya sha alwashin biyan miliyan daya kudin sadakinta

Auren Hanan Buhari, diyar shugaban kasa, ya zo da kalubale yayin da daya daga cikin manemanta ke kokarin kashe kansa, tashar tsakar gida ta ruwaito.

Ana shirin auren Hanan Buhari, daya daga cikin 'ya'yan shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari.

Rahotanni na nuna cewa, diyar shugaban kasar na shirin zama amaryar Muhammad Turad.

Muhammad Turad, tsohon mai bai wa tsohon gwamnan jihar Legas shawara na musamman, kuma ministan ayyuka a yanzu, Babatunde Fashola ne.

Hakazalika, Muhammad Turad da ne ga Honarabul Mahmud Sani Sha'aban, tsohon dan majalisar wakilai da ya wakilci mazabar Zaria a tsakanin 2003 zuwa 2007.

Honarabul Sha'aban ya yi takarar kujerar gwamna a jihar Kaduna a karkashin inuwar tsohuwar jam'iyyar ACN.

Ana sa ran daura auren Muhammad Turad da Hanan Buhari a ranar Juma'a, hudu ga watan Satumban 2020.

Ana tsaka da haka, wasu rahotanni ke bayyana daga jihar Kano cewa wani matashi ya sha alwashin kashe kansa matukar bai samu damar auren diyar shugaban kasan ba.

Matashin mai suna Kwamared Abba Ahmed, dan kasuwa ne kuma dalibi ne da ke shekarar karshe a jami'ar North West da ke Kano.

Kano: Matashi ya sha alwashin kashe kansa ranar auren Hanan Buhari
Kano: Matashi ya sha alwashin kashe kansa ranar auren Hanan Buhari. Hoto daga Sahara Reporters
Asali: Twitter

KU KARANTA: Bidiyon sojojin Najeriya suna yi wa tsoho duka tare da saka shi shiga kwata

Ya yi alkawarin bada sadakin naira miliyan daya tare da bada dubu dari biyu ga duk wanda ya hada su.

Sai dai a halin yanzu, an tabbatar da cewa matashin na kwance a gadon asibiti tun bayan da ya yanke jiki ya fadi yayin da ya samu labarin auren diyar shugaban kasar.

A yayin da Kwamared Abba ke kwance a gadon asibiti rai a hannun Allah, shi kuma Bashir Abdullahi, wanda ya sha alwashin bada shanu dari da hamsin a matsayin sadakinta, ya wallafa bidiyo inda yace ya karba kaddarar.

Matashin bai yi kasa a guiwa ba, ya kara da bada kyautar shanu hamsin domin a yi shagalin bikin diyar shugaban kasar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel