Zamu siya rigakafin cutar Korona guda biliyan biyu don baiwa yan Najeriya - Gwamnatin Buhari

Zamu siya rigakafin cutar Korona guda biliyan biyu don baiwa yan Najeriya - Gwamnatin Buhari

Gwamnatin tarayya ta ce tana hada kai da manyan kamfanonin da ke gudanar da bincike kan rigakafin cutar Korona a fadin duniya.

Ministan Lafiya, Dr Osagie Ehanire, ya bayyana hakan a Abuja ranar Alhamis yayin hirar manema labarai da kwamitin fadar shugaban kasa kan yaki da cutar Korona.

Ya ce Najeriya na shirin samun kwayar rigakafin bilyan biyu muddin aka samu.

"Najeriya na aiki da hukumar lafiyan duniya domin samun damar shiga manhajar ACT, wata manhaja ce da ke taimakawa wajen bibiya da daukan nauyin kamfanonin da ke shirin samar da rigakafin cutar COVID-19." Ehanire yace.

"Hakazalika muna da ra'ayin shiga tsarin COVAX, wani shiri ne na samun daman sayan rigakafin ana samu, musamman kasashe maras arziki."

"Wannan zai baiwa Najeriya daman samun kwayan rigakafin guda bilyan biyu don kare muradun kasashe maras arziki."

Zamu siya rigakafin cutar Korona guda bilyan biyu don baiwa yan Najeriya - Gwamnatin Buhari
Zamu siya rigakafin cutar Korona guda bilyan biyu don baiwa yan Najeriya - Gwamnatin Buhari
Asali: UGC

A bangare guda, hukumar takaita yaduwan cututtuka a Najeriya NCDC, kawo daren Laraba yan Najeriya sama da 50,000 suka kamu da cutar Korona kuma kimanin 1,000 sun mutu.

A jiya Laraba, NCDC ta bayyana cewa annobar Covid-19 ta sake harbin sabbin mutane 593 a fadin Najeriya.

Hakan na kunshe ne a cikin sanarwar da hukumar NCDC ta fitar da misalin karfe 11:29 na daren ranar Laraba 19 ga Agusta, 2020.

A cikin sanarwar da NCDC ta a shafinta na Twitter, ta bayyana yadda wadanda suka kamu a jihohin Najeriya kamar haka:

Plateau-186

Lagos-172

FCT-62

Oyo-27

Delta-25

Rivers-20

Ondo-19

Edo-18

Kaduna-17

Enugu-12

Akwa Ibom-10

Ogun-7

Abia-6

Gombe-6

Kano-3

Alkalluman da hukumar ta dakile cututtukan ta fitar a ranar Laraba 19 ga Agusta shekarar 2020 ya nuna cewa jimillar wadanda suka kamu da cutar ta korona a kasar 50,488 .

An sallami mutum 37,304 bayan an tabbatar da sun warke sarai, a yayin da cutar ta hallaka jimillar mutane 985.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel