Wawurar dukiya : EFCC tana bincikar ministan Buhari da wani daraktan ma'aikatarsa
Hukumar yaki da rashawa tare da hana yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC), ta ce tana bincikar zargin da ake wa Godswill Akpabio, ministan harkokin Neja Delta a kan rashawa.
A wata wasikar martani da ta fitar mai kwanan wata 14 ga Augusta ga gidauniyar 'yanci da shugabanci nagari, Adebayo Adeniyi, shugaban sashin tattalin arziki na EFCC, ya ce ana bincikar Kemebradikumo Pondei, mukaddashin manajan daraktan NDDC.
Kungiya mai zaman kanta, ta samu shugabancin Deji Adeyanju, mai rajin kare hakkin dan Adam, wanda ya bukaci EFCC da ta binciki Akpabio da Pondei a kan zargin rashawa da ake musu a NDDC.
"Mun rubuto wasikar nan ne don mu sanar da ku cewa mun samu kokenku mai kwanan wata 3 ga Augusta kuma muna sanar da ku cewa mun fara bincike," EFCC ta sanar a wata wasika.
"A saboda haka, ana bukatar ku da halartar wata tattaunawa a ranar Alhamis, 20 ga watan Augustan 2020 a hedkwatar EFCC, hawa na uku," yace.

Asali: Twitter
KU KARANTA: Da rana tsaka 'yan Indiya ke lalata da ma'aikata mata - Ma'aikatan kamfanin Atiku
Majalisar dattawan kasar nan ta kaddamar da bincike a kan zargin waddaka da N40 biliyan da kwamitin rikon kwarya na NDDC suka yi.
Pondei ya fadi sumamme a yayin da yake amsa tambayoyi daga kwamitin majalisar wakilai a daya daga cikin zamanta na binciken.
Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya kwatanta zargin da ake wa jami'an NDDC a matsayin cin amanarsa da suka yi., jaridar The Cable ta ruwaito.
Buhari ya ce za a bincike dukkan jami'an gwamnati na yanzu da wadanda suka shude.

Asali: Twitter
A wani labari na daban, mukaddashin shugaban ma’aikatar NDDC mai kula da cigaban Neja-Delta, Kemebradikumo Pondei, ya yi magana game da abin da ya faru da shi kwanaki.
Kwanakin baya Farfesa Kemebradikumo Pondei ya sume a yayin da ya ke amsa tambayoyi a gaban ‘yan majalisa, wasu su na ganin akwai alamun tambaya game da sumar.
Kemebradikumo Pondei ya yi magana da jaridar Vanguard a ranar Talata, ya ce wani irin mummunan ciwo ne ya auko masa lokacin da ya ke gaban ‘yan majalisa.
"Na samu wani irin ciwo ne da ban san kan shi ba da ya mamaye ni. Abin mamaki ne wasu su rika tunanin sumar karya na ke yi.” Inji Farfesa Kemebradikumo Pondei
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng