'Yan bindiga sun sace 'yan kasashen waje a Niger – 'Yan sanda

'Yan bindiga sun sace 'yan kasashen waje a Niger – 'Yan sanda

Rundunar 'Yan sandan jihar Niger ta tabbatar da cewa wasu da ake zargin 'yan bindiga ne sun sace wani dan kasan waje da yan Najeriya a tsakanin kauyukan Yankila da Regina a karamar hukumar Rafi ta jihar.

Adamu Usman, kwamishinan yan sandan jihar ne ya tabbatar da afkuwar lamarin yayin hirar da kamfanin dillancin labarai ta Najeriya, NAN, ta yi da shi a ranar Talata a garin Minna.

Usman ya ce a ranar 17 ga watan Agusta kimanin karfe 11.05 mun samu rahoton cewa 'yan bindiga sun kai hari sun sace ma'aikatan kamfanin gine gine ta Transparent.

An sace 'yan kasashen waje da ke aikin titi a Niger – 'Yan sanda
An sace 'yan kasashen waje da ke aikin titi a Niger – 'Yan sanda
Asali: Twitter

Ya ce wadanda ake sace din suna kula da aikin gyaran wuraren da suka lalace ne a titunan gwamnatin tarayya a jihar.

DUBA WANNAN: Terkimbi Ikyange: Tsohon Kakakin Majalisar Benue zai dawo APC

"Ba su sanar da rundunar yan sanda cewa suna aiki a jihar ba. Wannan abin da ya faru ne yasa muka san cewa suna jihar.

"Tuni mun aike da tawagar jami'an mu domin a ceto wadanda aka sace," a cewar Mr Usman.

A wani labarin da Legit.ng Hausa ta wallafa, Rundunar yan sandan jihar Akwa Ibom ta ce ta kama wata Mrs Mmayen Odiuotip, mai shekaru 39 fasto a cocin Land of Testimony Ministry a kan zarginta da satar jinjira.

Cocin yana Marina Road ne a karamar hukumar Oron na jihar kamar yadda The Punch ta ruwaito. Mai magana da yawun 'yan sandan jihar, CSP Nnudam Fredrick, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar a babban birnin jihar, Uyo.

Ya ce wasu da ake zargi da hannu cikin satar yaran sun hada da Esther Esin, 41 yar garin Eyo Abasi, a karamar hukumar Oron, Mrs Rose Asuquo, 32, yar garin Mbak Atai, karamar hukumar Itu, da Ubong Akpan, 42, dan garin Mbak Atai, daga karamar hukumar Itu.

Saura sun hada da Mr Samuel Idobo, 40, mazaunin Ikot Asukpong, a karamar hukumar Ibiono Ibom da Mrs Eno Peter, 40, yar garin Ikot Andem Itam, da ke karamar hukumar Itu.

"Jajircewar da rundunar yan sandan ke yi domin magance matsalar satar yara ya fara samun nasara inda aka damke gawurtattun masu satar yara a jihar," in ji Fredrick.

Fredrick ya ce an yi nasarar kama yan kungiyar masu satar yaran ne sakamakon sahihan bayannan sirri da rundunar ta samu a watan Yuni.

Ya ce shugaban kungiyar, Rose Ekpenyong, ta hada baki da sauran wadanda aka ambaci sunansu a matsayin wadanda ake zargi wurin sayar da wata jinjira a shekarar 2018.

Fredrick ya ce faston ta amsa laifin ta inda ta ce an saya jinjiran ne domin a bawa yar uwar ta mai suna Esin.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel