'Ina da hujjoji na yadda aka yi sama da fadi da N6.25bn da aka turawa NDDC na tallafin COVID-19'

'Ina da hujjoji na yadda aka yi sama da fadi da N6.25bn da aka turawa NDDC na tallafin COVID-19'

Shugaban kwamitin rarraba tallafin COVID-19 na hukumar bunkasa Niger Delta (NDDC), Sobomo Jackrich ya yi ikirarin cewa yana da hujjoji na yadda aka sace N6.25bn daga asusun hukumar, kudaden da ya kamata a raba na tallafin COVID-19.

Sai dai ya karyata zargin da ake yi na cewar ya yi zargin ne don damfarar kwamitin mulki na hukumar karkashin shugabancin Farfesa Keme Pondei.

Jackrich, a cikin wata sanarwa a Fatakwal, a karshen mako ya bukaci kwamitin IMC da su daina wannan zargi, kuma su shirya kare kansu gaban majalisar tarayya.

Ya jaddada cewa yana da hujjoji kwarara akan duk zargin da ya yi.

Ya magantu akan zargin da kwamitin IMC ya yi, yana mai cewa abun takaici ne yadda hukumar ke kwatantashi da karen farauta na kwamitin rarraba tallafin hukumar.

Ya bayyana cewa IMC ya gaza karyata ikirarin nasa, yana mai cewa yana da hujjojin yadda IMC ke biyan 'yan kwangilar bogi kudaden yin aiki, duk don sace kudaden.

KARANTA WANNAN: FG ta gargadi masu bada cin hanci don kar ayi masu gwajin COVID-19 a tashar jirgin sama

'Ina da hujjoji na yadda aka yi sama da fadi da N6.25bn da aka turawa NDDC na tallafin COVID-19'
'Ina da hujjoji na yadda aka yi sama da fadi da N6.25bn da aka turawa NDDC na tallafin COVID-19'
Asali: UGC

Ya ce: "Kokarin hukumar NDDC na kare kwamitin IMC abun takaici ne, ko dai suna yi ne a jahilci ko kuma suna son boye gaskiya ne.

"Zai fi kyau NDDC ta bari IMC ta kare kanta a gaban kwamitin bincike na majalisar tarayya, domin kuwa ina da hujjoji na dukkanin zarge zargen da nayi.

"A wannan lokaci, dole IMC ta yi bayani kwabo bayan kwabo na yadda aka raba N6.25bn da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ba hukumar na tallafin COVID-19.

"Duk wani ikirari da IMC ke yi na cewar ta sayi kayan aiki na yaki da cutar, ya zama karyar banza, kuma basu rabawa mutane tallafin komai ba, suna farfagandar karya ne kawai."

Sobomo Jackrich ya bayyana cewa shuwagabannin ilimi, kiwon lafiya da walwalar jama'a na hukumar, suna son yin rufa rufa akan wannan tonon silili.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel