Adadin masu cutar korona a Najeriya ya zarta 47,000 - NCDC

Adadin masu cutar korona a Najeriya ya zarta 47,000 - NCDC

Babu shakka mahukuntan lafiya na ci gaba da fadi tashin dakile yaduwar cutar korona a Najeriya, sai dai fa lamarin ya ci tura domin kuwa cutar na ci gaba da bazuwa babu sassauci.

A halin yanzu an samu bullar cutar covid-19 a duk jihohi 36 na Najeriya da kuma babban birnin tarayya kamar yadda alkaluman cibiyar dakile yaduwar cututtuka a kasar NCDC suka tabbatar.

Taskar bayanai ta NCDC a ranar Laraba, 12 ga watan Agustan 2020, ta sanar cewa cutar korona ta harbi mutane 47,743 yayin da mutum 33,943 suka samu waraka.

Shugaban NCDC; Chikwe Ihekweazu
Shugaban NCDC; Chikwe Ihekweazu
Asali: Twitter

Ya zuwa yanzu dai mutane 956 cutar ta hallaka a fadin Najeriya kamar yadda hukumar NCDC ta fidda bayanan alkalumanta.

Rumbun tattaro bayanai na NCDC ya nuna cewa, an yi wa mutum 338,084 gwajin cutar a duk fadin kasar tun bayan bullarta karo na farko a ranar 27 ga watan Fabrairun 2020.

Haka kuma alkaluman cibiyar dakile cututtuka ta kasar sun nuna cewa, mutum 12,844 ne suka rage masu dauke da kwayoyin cutar.

KARANTA KUMA: Bayan yi wa Sarki Salman tiyata, an garzaya da shi yankin Bahar Maliya inda zai huta

Da misalin karfe 11.29 na jiya Laraba da daddare, NCDC ta sanar da cewa an gano karin sabbin mutane 453 da cutar ta harba a fadin Najeriya.

Sabbin mutane 453 da cutar ta harba cikin jihohi 16 sun kasance kamar haka:

Lagos(113), Abuja(72), Filato(59), Enugu(55), Kaduna(38), Ondo(32), Osun(26), Ebonyi(20), Ogun(9), Delta(8), Borno(7), Akwa Ibom(6), Oyo(5), Bauchi(1), Kano(1) da Ekiti(1).

Har kawo yanzu jihar Legas ce a kan sahu na gaba ta fuskar yawan mutanen da cutar ta harba, sai kuma birnin Abuja a mataki na biyu yayin da jihar Oyo ta biyo bayansu a mataki na uku.

Ga jerin adadin mutanen da cutar ta harba cikin kowace daya daga cikin jihohi 36 na Najeriya da cutar ta bulla:

Lagos - 16,187

Abuja - 4,597

Oyo - 2,895

Edo - 2,399

Ribas - 1,972

Kaduna 1,666

Kano - 1,644

Filato - 1,643

Delta - 1,621

Ogun - 1,506

Ondo - 1,356

Enugu - 969

Ebonyi - 908

Kwara - 882

Katsina - 746

Borno - 697

Osun - 678

Abia - 663

Gombe - 635

Bauchi - 579

Imo - 485

Benue - 430

Nasarawa - 371

Bayelsa - 346

Jigawa - 322

Akwa Ibom - 241

Niger - 226

Ekiti - 194

Adamawa - 185

Anambra - 156

Sokoto - 154

Kebbi - 90

Taraba - 78

Zamfara - 77

Cross River - 73

Yobe - 67

Kogi - 5

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel