Bayan yi wa Sarki Salman tiyata, an garzaya da shi yankin Bahar Maliya inda zai huta

Bayan yi wa Sarki Salman tiyata, an garzaya da shi yankin Bahar Maliya inda zai huta

Kamfanin dillancin Labarai na kasar Saudiya SPA ya ruwaito cewa, Sarki Salman Bin Abdul’aziz, ya isa yankin Bahar Mahaliya domin samun hutu bayan tiyata da aka yi masa a mafitsara.

Sarkin wanda ya shekara 84 a duniya, an sallamo shi daga wani asibitin birnin Riyadh a ranar 30 ga watan Yuli, bayan samun nasarar yi masa tiyata.

A halin yanzu zai ci gaba da shakatawa domin samun nutsuwa a wani gari mai suna Neom wanda dansa, Yarima Muhammad yake ci gaba da ginawa a Arewa maso Yammacin kasar ta Saudiya.

Ana dai yi wa Yarima Salman mai shekaru 34 a duniya kallon mai rike da akalar jagorancin kasar musamman a yayin da rashin lafiya ta addabi mahaifinsa da kuma tsufa da ya cimma sa.

Sarki Salman
Hoto daga jaridar Daily Nigerian
Sarki Salman Hoto daga jaridar Daily Nigerian
Asali: Twitter

A wani rahoto mai nasaba da wannan da jaridar Legit.ng ta ruwaito makonni da suka shude, an samu nasarar yi wa Sarki Salman tiyata a mafitsara a babban asibitin Sarki Faisal da ke birnin Riyadh.

Sarki Salman wanda shi ne shugaban masu kula da Masallatan Harami biyu da ke Kasar Saudiya, ya nuna godiyarsa ga duk wadanda suka kira ko aiko masa da sakon fatan alheri.

Babu shakka shugabannin kasashen duniya da dama sun rika aike wa da Sarkin sako na fatan samun waraka cikin gaggawa, ciki har da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.

Wannan sako yana kunshe cikin wata sanarwa da hadimin shugaban kasa, Mallam Garba Shehu ya sanya wa hannu kamar yadda jaridar Daily Nigerian ta ruwaito.

KARANTA KUMA: Sai duhun dare ya kawo Mata ke zuwa karbar maganin tsarin iyali a Bauchi - Bincike

Shugaban ya ce: "A madadi na, gwamnati da jama'ar Najeriya, ina yin addu'ar fatan alheri da kuma samun sauki ga Sarkin Saudiyya, daya daga cikin mafi kyawun shugabannin da na taba haduwa da su a yayin mu'amala da shugabannin duniya."

"Sarki Salman aboki ne na kwarai wanda ya bai gaza wajen tabbatar da Najeriya a kowane lokaci ta hanyar hadin gwiwa da aiki tare."

"A yayin da Sarkin yake samun kulawa a asibiti, ina masa fatan alheri da addu'o'in samun lafiya cikin gaggawa."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel