Boko Haram: Bayan tuhumar Mailafiya, ya janye kalamansa ga gwamnonin arewa

Boko Haram: Bayan tuhumar Mailafiya, ya janye kalamansa ga gwamnonin arewa

Bayan amsa gayyatar hukumar jami'an tsaro ta farin kaya, tsohon gwamnan bankin Najeriya, Dr. Obadiah Mailafiya, ya janye ikirarin da yayi na farko.

Idan za mu tuna, a wata tattaunawa da aka yi sa Mailafiya a wani gidan rediyo na Abuja, tsohon mataimakin gwamnan babban bankin Najeriya, ya zargi daya daga cikin gwamnonin arewa da zama kwamandan Boko Haram a Najeriya.

A ranar Laraba, kungiyar gwamnonin arewa kuma gwamnan jihar Filato, Simon Lalong, ya kwatanta wannan zargi da babba.

Ya ce wannan ikirarin ko dai siyasa ne ko kuma wani yunkurin na sare wa gwamnonin guiwa duk da kokarin da ake yi na ganin yakar ta'addanci.

A yayin zantawa da manema labarai a garin Jos, bayan amsa tambayoyi da Mailafiya ya yi, ya ce ba a fahimci zantukansa bane. Ya yi mamakin yadda za a yanke masa hukunci a cikin hirar da yayi ta minti 55.

Boko Haram: Bayan tuhumar Mailafiya, ya janye kalamansa ga gwamnonin arewa
Boko Haram: Bayan tuhumar Mailafiya, ya janye kalamansa ga gwamnonin arewa. Hotodaga Daily Nigerian
Asali: Facebook

KU KARANTA: Na siyar da jinjirina ne don biyan kudin asibitin matata - Magidanci

"Tabbas ni na sanar da hakan amma a dukkan hirar minti 55 muka yi. Abinda na fada ne ba a fahimta ba.

"Wannan lokacin ba shine na musanta abinda nace ba. Tabbas na fitar da wasu bayanai masu matukar hatsari ga jama'a," yace.

Kamar yadda Mailafiya yace, bayanan da ya tara ya samo su ne daga wasu majiyoyi da bai tabbatar ba.

"Da na yi taka-tsan-tsan wurin tattara bayanan da na samu amma kuma wasu ban nemi karin bayani ba," ya sanar.

Mailafiya ya jinjinawa jami'an tsaro na farin kaya a kan yadda suka karbesa cike da kwarewa da adalci.

A wata takarda da aka fitar a garin Jos, Dr. Mukut Simon Macham, daraktan yada labarai da sadarwa na shugaban kungiyar kuma gwamnan jihar Filato, Simon Bako Lalong, ya ce kungiyar gwamnonin arewa ta matukar damuwa da wannan zargi mai girma na Mailafiya, wanda dole ne a bincika da gaggawa.

Takardar ta ce kungiyar, wacce ke aiki tare da gwamnatin tarayya, jami'an tsaro, yankuna, kungiyoyin farar hula, sarakunan gargajiya da na addinai, don kawo karshen ta'addanci a yankin, tana bukatar bincikar ikirarin.

Ta kara da cewa: "A matsayin mu na gwamnonin arewa, mun yi taruka babu adadi don tattaunawa a kan rashin tsaron da ya addabi yankin arewa da kasar baki daya.

"Muna kushe duk al'amuran ta'addanci kamar Boko Haram, 'yan bindiga, 'yan fashi da makami, garkuwa da mutane da sauransu.

"Muna saka jami'an tsaro da shugaban kasa don kawo karshen wannan matsalar.

"Cewa daya daga cikinmu yana jagorantar Boko Haram a Najeriya babban zargj ne wanda ba za mu bar shi haka ba. Muna bukatar a gaggauta bincike mai tsanani a kai."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel