El-Rufai yakamata DSS su gayyata, ba Mailafiya ba - Reno Omokri

El-Rufai yakamata DSS su gayyata, ba Mailafiya ba - Reno Omokri

Tsohon mai magana da yawun shugaban kasa, Reno Omokri, ya yi martani a kan rahoton hukumar jami'an tsaro ta farin kaya na gayyatar tsohon mataimakin shugaban bankin Najeriya, Obadiah Mailafiya, a kan ikirarin cewa wani gwamnan arewa ne kwamandan Boko Haram.

A wallafar da ya yi a shafinsa na Twitter, Reno Omokri ya ce kamata yayi hukumar jami'an tsaro ta farin kaya ta gayyaci Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna.

Kamar yadda yace, "Duk wanda yake tunanin Obadiah Mailafia yana terere ne, toh ya duba wasu kanun labarai daga 2012 da 2014.

"Mailafia ba wani abu yake cewa ba da makiyaya da kuma 'yan Boko Haram basu cewa. Wannan ne yasa Muhammadu Buhari ke sako tubabbun 'yan Boko Haram tare da yi musu gata.

"Gwamna Nasir El-Rufai ya amsa biyan makiyaya masu kisa a Kaduna ta kudu don su daina kashe-kashe."

"Wannan ikirarin na shi ya ci karo da dokar hana ta'addanci ta shekarar 2011. Idan da ace akwai doka a Najeriya, ya kamata a ce El-Rufai yana gidan yari ne ba gidan gwamnati.

"Wasu na cewa kalaman Mailafiya za su hargitsa Najeriya ta koma tamkar Rwanda. Bayyana gaskiya ba za ta mayar da Najeriya Rwanda ba.

"Abinda ke faruwa a kudancin Kaduna tuni ya yi kama da kashe-kashen da ake yi a Rwanda. Makiyaya na kashe kiristoci kuma El-Rufai na biyansu. Me kuke kiran wanann," ya wallafa.

El-Rufai yakamata DSS su gayyata, ba Mailafiya ba - Reno Omokri
El-Rufai yakamata DSS su gayyata, ba Mailafiya ba - Reno Omokri. Hoto daga shafin Linda Ikeji
Asali: Twitter

KU KARANTA: Zamfara: Kotu ta yankewa soja hukuncin shekaru 55 a kan kisan farar hula

A wani labari na daban, kungiyar gwamnonin arewa a ranar Laraba ta yi kira ga cibiyoyin tsaro da su binciki zargin da tsohon mataimakin shugaban bankin Najeriya, Dr. Obadiah Mailafiya, na cewa "daya daga cikin gwamnonin arewa ne kwamandan Boko Haram a Najeriya".

A wata takarda da aka fitar a garin Jos, Dr. Mukut Simon Macham, daraktan yada labarai da sadarwa na shugaban kungiyar kuma gwamnan jihar Filato, Simon Bako Lalong, ya ce kungiyar gwamnonin arewa ta matukar damuwa da wannan zargi mai girma na Mailafiya, wanda dole ne a bincika da gaggawa.

Takardar ta ce kungiyar, wacce ke aiki tare da gwamnatin tarayya, jami'an tsaro, yankuna, kungiyoyin farar hula, sarakunan gargajiya da na addinai, don kawo karshen ta'addanci a yankin, tana bukatar bincikar ikirarin.

Ta kara da cewa: "A matsayin mu na gwamnonin arewa, mun yi taruka babu adadi don tattaunawa a kan rashin tsaron da ya addabi yankin arewa da kasar baki daya.

"Muna kushe duk al'amuran ta'addanci kamar Boko Haram, 'yan bindiga, 'yan fashi da makami, garkuwa da mutane da sauransu.

"Muna saka jami'an tsaro da shugaban kasa don kawo karshen wannan matsalar.

"Cewa daya daga cikinmu yana jagorantar Boko Haram a Najeriya babban zargj ne wanda ba za mu bar shi haka ba. Muna bukatar a gaggauta bincike mai tsanani a kai."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel