Dr. Isa Pantami ya kammala manyan ayyuka 11 da zasu farfado da tattalin arziki

Dr. Isa Pantami ya kammala manyan ayyuka 11 da zasu farfado da tattalin arziki

Ministan sadarwa da tattalinn arzikin zamani, Dr. Isa Pantami, ya bude sabbin ayyuka guda goma sha daya, wanda kashi na biyu na ayyukan da aka kammala na tattalin arziki ta yanar gizo.

Ayyukan, wadanda aka yi su a sassa daban daban na kasar, an bude su ne a wani taro a ranar Talata ta yanar gizo, da kudurin fadada hanyoyin tattalin kasar.

Da kuma tabbatar da tsaro da yaki da cin hanci da rashawa ta hanyar kimiyyar bayanan watsa labarai (ICT) da kuma kawo gyare gyare a sadarwar wayoyin salula.

Za a iya tunawa a ranar Alhamis, 23 ga watan Yuli, 2020, Minista Dr. Pantami ya bude ayyuka shida da aka kammalasu a sassa na kasar domin fadada sadarwar kasar.

Ayyukan da aka bude anyi su ne karkashin hukumar sadarwa ta Nigeria (NCC), hukumar bunkasa kimiyyar sadarwa ta kasa (NITDA), hukumar karba da aika sako ta Nigeria (NIPOST).

KARANTA WANNAN: Zaben Nasarawa: Yadda masu zabe suka dinga sayar da kuri'a a kan N500 - YIAGA ta fasa kwai

Dr. Isa Pantami ya kammala manyan ayyuka 11 da zasu farfado da tattalin arziki
Dr. Isa Pantami ya kammala manyan ayyuka 11 da zasu farfado da tattalin arziki
Asali: Facebook

Sai kuma asusun USPF, wadanda gaba dayansu suke karkashin ma'aikatar sadarwa da tattalin arziki ta yanar gizo, karkashin shugabancin Dr. Pantami.

Ayyaukan da aka bude sune:

- Cibiyar ilimin manyan makarantu (TIKC), jihar Delta.

- Sabon ofishin karba da aika sako, jihar Delta.

- Sabunta cibiyar musayar wasikun yanar gizo ta kasa (NMEC), jihar Bayelsa.

– Cibiyar raba bayanan kiwon lafiya ta yanar gizo, jihar Bauchi.

– Cibiyar rubuta jarabawar kai tsaye ta yanar gizo, jihar Borno.

– Cibiyar karfafa guiwar fasahar bayanai, jihar Kogi.

– Cibiyar horaswa kan fasarar bayanai, jihar Jigawa.

– Cibiyar horaswa kan fasarar bayanai, jihar Imo.

– Cibiyar sadarwar gaggawa (ECC) Ilorin, jihar Kwara.

– Cibiyar sadarwar gaggawa (ECC) Calabar, jihar Cross River

– Cibiyar ilimin makarantu (SKC), jihar Gombe.

Za a iya tunawa a ranar Alhamis, 23 ga watan Yuli, 2020, Minista Dr. Pantami ya bude ayyuka shida da aka kammalasu a sassa na kasar domin fadada sadarwar kasar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel