Sanatoci 10 da suka shafe shekara ba tare da gabatar da kudiri ko daya ba a majalisa

Sanatoci 10 da suka shafe shekara ba tare da gabatar da kudiri ko daya ba a majalisa

Shugaban majalisar dattawa, Sanata Ahmad Lawan da kuma tsohon gwamnan Kano, Mallam Ibrahim Shekarau (APC, Kano), na daga cikin jerin sanatoci 10 da suka shafe shekara guda cur ba tare da gabatar da kudiri ko daya ba.

Tabbas sashe na 4 cikin kundin tsarin mulkin kasa da aka yi wa kwaskwarima tun a shekarar 1999, ya rataya wa ‘yan majalisun tarayya nauyin gabatar da kudirorin samar da dokar zaman lafiya, da shugabanci nagari a kasar.

Nauyi na farko da ya rataya wuyan kowane dan majalisar shi ne gabatar da kudirin doka da zai yi daidai da bukatun al’ummomin da suke wakilci tare da sa ido kan yadda ake tafiyar da al’amura a Ma’aikatu, Cibiyoyi da Hukumomin Gwamnati.

Shugaban Majalisar Dattawa; Sanata Ahmad Lawan
Shugaban Majalisar Dattawa; Sanata Ahmad Lawan
Source: Facebook

A ranar 11 ga watan Yunin 2019 ne aka rantsar da sabuwar Majalisar Dattawa ta 9 a tarihin Najeriya, kuma tun daga wancan lokaci kawo yanzu, an gabatar da kudirori fiye da 450 kamar yadda binciken jaridar Daily Trust ya nuna.

Sauran Sanatocin da suka shafe shekara guda suna dumama kujera ba tare da gabatar da kudiri ko daya ba sun hadar da; Adamu Bulkachuwa (APC, Bauchi), Christopher Stephen Ekpenyong (PDP, Akwa Ibom), da Godiya Akwashiki (APC, Nasarawa).

Ragowar sun kunshi; Emmanuel Yisa Orker-jev (PDP, Benue), Kabir Abdullahi Barkiya (APC, Katsina), Nicholas Olubukola Tofowomo (PDP, Ondo), Peter Onyeluka Nwaoboshi (PDP, Delta) and Lawali Hassan Anka (PDP, Zamfara).

Sanata Ignatius Datong Longjan (APC, Plateau) da kuma Sanata Sikiru Adebayo Osinowo (APC, Lagos) ba su gabatar da kudiri ko daya har zuwa lokacin da mai yankan kauna ta katse musu hanzari a waran Fabrairu da Yunin 2020 jere.

KARANTA KUMA: Mutanen da cutar korona ta harba a Najeriya sun zarta 46,000 - NCDC

A yayin da Shugaban majalisar bai ce komai ba dangane da yadda hakan ta kasance yayin da manema labarai suke nemi jin ta bakinsa, shi kuwa Sanata Shekarau ta ce kudirin da zai gabatar kan dokar fansho yana na tafe ba jimawa.

Haka kuma Sanata Adamu Muhammadu Bulkachuwa (APC, Bauchi North), ya ce bai gabatar da kudiri ko daya ba a karan kansa, amma ya yi tarayya da wasu sanatocin wajen gabatar da kudirori da dama.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Tags:
Online view pixel