Hadin gwiwar dakarun soji: Kwararre ya yi hasashen ta'addanci zai zamo tarihi a Najeriya ba jimawa

Hadin gwiwar dakarun soji: Kwararre ya yi hasashen ta'addanci zai zamo tarihi a Najeriya ba jimawa

- An yaba wa shugaban hafsan sojin sama da na kasa yayin da suka kaddamar da sabuwar dabara ta aikin hadin gwiwa

- Wannan yabo ya fito ne daga wani sananne kwararre kan sha’anin tsaro Terrence Kuanum

- Kuanum ya ce irin wannan aiki na hadin gwiwa da hafsoshin sojin suka kawo zai kawo karshen tayar da kayar baya a yankin Arewa maso Gabashin kasar

Wani sananne masanin harkokin tsaro, Terrence Kuanum, ya zayyana cewa sauran kiris ta’addancin masu tayar da kayar baya a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya ya zamto tarihi.

Kuanum ya fadi hakan yayin yabawa dabarar aikin hadin gwiwa da shugaban hafsan sojin kasa, Tukur Buratai da takwaransa na sojin sama, Abubakar Sadique suka kaddamar.

Ya ce wannan sabuwar dabara za ta kawo karshe duk wani nau’i na ta’addanci a Najeriya.

Furucin Kuanum ya zo yayin da yake zantawa da manema labarai cikin birnin Abuja a ranar Asabar, 8 ga watan Agusta.

Kuanum ya ce ci gaba na baya bayan nan da ake samu a tsakanin dakarun soji na da matukar muhimmanci a fagen yaki da ‘yan tawaye.

Tukur Buratai da Abubakar Sadique
Tukur Buratai da Abubakar Sadique
Asali: UGC

Ya ce muddin aka inganta aikin hadin gwiwar da shugabanni hafsoshin sojin suka kaddamar kuma aka dore a kan hakan, to lallai zai kawo karshen duk wani nau’i na ta’adddanci a kasar.

A wani rahoto da Legit.ng ta ruwaito, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayar da umurnin yin garambawul a dukkanin bangarorin tsaro na kasar.

Mai bashi shawara kan tsaro na kasa Babagana Monguno ya bayyana hakan bayan fitowa daga taron majalisar tsaro a fadar shugaban kasa, Abuja.

Mista Monguno a ranar Talata bayan fitowa daga taron majalisar tsaro ta kasa, ya ce shugaba Buhari ya bada umurnin yin garambawul a bangarorin tsaro na Nigeria.

A yayin yiwa 'yan jarida karin haske, Munguno ya bukaci zaman lafiya, yana mai daukar alkawarin cewa shugaban kasa da hafsoshin tsaro zasu kawo karshen ta'addanci a Arewa.

KARANTA KUMA: Yajin Aiki: ASUU za ta koma teburin sulhu da Gwamnatin Tarayya

Ya ce bayan tattauna batutuwan da suka shafi tsaron kasar a wajen taron, an kuma tattauna batu kan safara da tu'ammali da miyagun kwayoyi.

A cewarsa, Najeriya ta tashi daga cibiyar hada hada, zuwa cibiyar sarrafa magungunan da ake safararsu, wanda babbar matsala ce.

Ya yi nuni da cewa a kwanakin baya an rufe gine ginen sarrafa magunguna guda 17 a fadin kasar tare da yin kira da a hada hannu wajen kawo karshen fatauci da shan miyagun kwayoyi.

Har ila yau a wajen taron, shuwagabannin rundunonin tsaro sun yiwa Buhari bayani kan hanyoyin da suke ganin ya kamata abi don kawo karshen ta'addanci a kasar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel