Ka yi amfani da kujerarka wurin kawo hadin kai a arewa - Matawalle ga Sarkin Kano

Ka yi amfani da kujerarka wurin kawo hadin kai a arewa - Matawalle ga Sarkin Kano

Gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle, ya yi kira ga sarkin Kano, Aminu Ado-Bayero, da ya yi amfani da kujerarsa wurin assasa hadin kai na yankin arewacin kasar nan.

Gwamnan ya yi wannan kiran ne ga sarkin yayin da ya kai ziyara gidan gwamnatin jihar a ranar sati, kamar yadda yake kunshe a wata takarda da mai bada shawara na musamman a kan fannin yada labarai ga gwamnan, Zailani Bappa, ya fitar.

Matawalle ya jaddada cewa arewa na matukar bukatar shugabanni da za su hada kan jama'a don komawa saiti daya na siyasa da al'adu.

"Mai martaba, arewa na bukatar shugabanninsu da za su hada kan jama'arta a siyasance da al'adance kamar baya," Matawalle ya ce.

Gwamnan ya danganta rashin hadin kan yankin da ci gaban rashin ganin girman sarakunan gargajiya.

Ka yi amfani da kujerarka wurin kawo hadin kai a arewa - Matawalle ga Sarkin Kano
Ka yi amfani da kujerarka wurin kawo hadin kai a arewa - Matawalle ga Sarkin Kano. Hoto daga Daily Nigerian
Asali: Twitter

KU KARANTA: Hotunan cikin gidan hamshakin mai kudin duniya da za a iya cire gidaje 18,000

Ya tuna cewa, a baya jama'a suna mutunta masarautun gargajiya a kan yadda suke bada gudumawa wurin hadin kan al'umma da zaman lafiya.

"Ina kira gareka da abokan aikinka a arewa da su samo hanyar aiki tare don farfado da hadin kan baya.

"Ina tabbatar muku da cewa, a bangarenmu zan yi amfani da matsayina don tabbatar da cewa nayi kira ga takwarorina wurin farfado da hadin kan baya," Gwamna Matawalle ya tabbatar.

Tun a farko, a ziyartar da Sarkin ya kaiwa gwamnan, ya ce ya zo ne don ganin sauran sarakunan jihar ballantana a wannan lokacin da ya shiga sahun magabatansa.

Sarkin ya jinjinawa Gwamna Matawalle a kan yadda ya dawo da zaman lafiya a jihar, ya tabbatar da cewa masarautarsa za ta yi addu'ar tabbatar zaman lafiya ga jama'a da kasar baki daya.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel