Yanzu: Kwaminitin gwamnonin Arewa maso Gabas sun fara ganawa a Maiduguri

Yanzu: Kwaminitin gwamnonin Arewa maso Gabas sun fara ganawa a Maiduguri

Rahotannin da Legit.ng Hausa ke samu yanzu daga jaridar The Nation na nuni da cewa kwamitin kwararru na gwamnonin Arewa maso Gabas (NEGF) na cin ganawa yanzu haka a Maiduguri, babban birnin jihar Borno.

Kwamitin kwararrun na NEGF ya kunshi sakatarori na gwamnatin kowacce jihar, cikin jihohi shida da suka hada Arewa maso Gabas.

Sauran mambobin kwamitin sun hada fda kwamishinonin harkokin jin kai da kai agajin iftila'i, sakatarorin din-din-din na jihohin shida, da kuma wakilai 6 daga hukumar NEDC daga jihar.

Wata majiya ta shaidawa jaridar The Nation cewa sakatarorin gwamnatin jihohin a wajen taron, ana saran zasu yi bitar taron da gwamnonin shiyyar suka yi a Gombe, watan da ya shude.

Ana sa ran za aci gaba da gudanar da taron gobe (Juma'a), akan manufa daya ta samar da makama kan taron gwamnonin da ake sa ran gudanarwa a ranar Asabar a Maiduguri.

Legit.ng ta ruwaito cewa, taron kungiyar da ta gabata, an tattauna ne kan matsalolin tsaro da ya addabi shiyyar, yawaitar marasa aikin yi da karancin tallafi daga hukumar bunkasa shiyyar Arewa maso Gabas NEDC.

KARANTA WANNAN: Rundunar sojin Nigeria ta sa hannu kan jarjejeniyar fara sarrafa kayan aikinta da kanta

Yanzu: Kwaminitin gwamnonin Arewa maso Gabas sun fara ganawa a Maiduguri
Yanzu: Kwaminitin gwamnonin Arewa maso Gabas sun fara ganawa a Maiduguri
Asali: Twitter

Rundunar sojin Nigeria a ranar Alhamis, ta sa hannu kan wata takardar jarjejeniya da kamfanin Super Green Security, da hukumar masana'antun tsaro ta Nigeria da kuma cibiyar injiniyoyi.

Ta kulla wannan yarjejeniyar ne domin fara sarrafa kayayyakin aikin da rundunar sojin take bukata da ma na fannin tsaron kasar baki daya.

Kulla yarjejeniyar na karkashin umurnin shugaban Buhari na 5 da aka sa a dokar 2018, da nufin bunkasa sarrafa kayan aiki ta hanyar amfani da ilimin kimiya da fasahar injiniyoyin kasar.

Idan za a tuna, a kokarin gwamnatin tarayya na tabbatar da cewa kowanne mutum ko kungiya sun sarrafa kayan aikinsu da kansu, rundunar sojin ta dauri damarar cimma hakan.

A baya rundunar ta sarrafa wasu ababen hawa na yaki da take amfani da su a matsayin ababen hawa masu kariyar EMRAP, motocin sintiri na TYP, da takalma, hulunan kwano da sauransu.

Babban shugaban hukumar masana'antun tsaro na kasa, Manjo Janar Victor Ezugwu yayin sanya hannu akan takardar ya jinjinawa shugabancin rundunar sojin na mayar da rundunar sojin kasar ta rinka sarrafa kayayyakin aikinta da kanta.

A cewar M.J Victor Ezuwgu wannan kokari na TY Buratai zai ragewa kasar kudaden da take kashewa wajen sayowa rundunar sojin kayayyakin da take amfani da su.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel