Fiye da jami'o'i 32 sun ba da gudunmuwar yaki da cutar korona a Najeriya - NUC

Fiye da jami'o'i 32 sun ba da gudunmuwar yaki da cutar korona a Najeriya - NUC

Hukumar da ke sa ido kan jami'o'in Najeriya NUC, ta ce akwai fiye da jami'o'i 32 a fadin kasar da suke taka rawar gani da manufar kawo karshen annobar korona.

NUC ta ce jami'o'i na ci gaba da fadi tashi wajen gudanar da bincike da nazarin shawo kan annobar korona wadda ta zamto ruwan daren da ya game duniya.

Babban sakataren hukumar NUC, Farfesa Abubakar Rasheed, shi ne ya sanar da hakan a wani taro na manema labarai dangane da gudunmuwar da jami’o’in kasar ke bayar wa wajen yaki da annobar korona.

Ya ce kididdigar alkaluman cibiyar tantance kwarewa ta Afirka, ta tabbatar da cewa binciken da manyan makarantu ke aiwatar da kuma ayyukan ci gaba na yiwuwa a Najeriya.

Hukumar NUC
Hoto daga Premium Times
Hukumar NUC Hoto daga Premium Times
Asali: Twitter

A cewarsa, "musamman binciken gano riga kafin cutar korona wadda Jami'ar Redeemers ke gudanarwa tare da hadin gwiwar jami'ar Cambridge ta Birtaniya."

Sauran jami'o'in da gudunmuwar ta fito fili sun hadar da Jami'ar Ahmadu Bello da ke Zariya, Jami'ar Bayero ta Kano, Jami'ar Legas, Jami'ar Benin, Jami'ar Fatakwal da kuma Jami'ar Jos.

Wannan jami'o'in sun hidimantu wajen gudanar da gwajin tantance masu dauke da kwayoyin cutar ta Covid-19 a fadin kasar.

Haka hukumar NUC ta ce ta fara tattaro bayanai daga jami’o’i a fadin kasar domin tabbatar da shirinsu na komawa bakin aiki.

Hukumar ta ce ana ci gaba da fafutikar kawo karshen yajin aikin da kungiyar malaman jami’o’i ta ASUU ke faman yi tun tsawon watanni da dama da suka gabata kawo yanzu.

NUC ta ce yajin aikin da kungiyar ASUU ke yi na baranza tare da taka rawa wajen kawo tsaiko a harkokin karatu a jami’o’in kasar.

Ana iya tuna cewa tun a watan Maris gwamnatin tarayya ta ba da umarnin rufe kafatanin makarantu manya da kanana a sakamakon barkewar annobar korona.

KARANTA KUMA: Samari 3 sun mutu a hatsarin tsakar dare

A cewar Farfesa Rasheed wanda mataimakinsa Suleiman Yusuf ya wakilta a taron wanda aka gudanar a ranar Talata cikin birnin Abuja, NUC na ci gaba da fadi-tashi tare da jami’o’i da tattaunawa a kan matakan da za a shimfida gabanin komawa aiki.

Ya ce jami’o’in da bas a karkashin jagorancin kungiyar ASUU za su iya komawa bakin aiki da zarar dukkan matakan da aka shata sun tabbata kuma an kiyaye su.

A ranar 9 ga watan Maris ne kungiyar ASUU ta shiga yajin aiki na gargadi, inda kuma a ranar 23 ga watan Maris ta zarce da na sai mama ta gani.

ASUU ta shiga yajin aikin ne a sakamakon rashin biyan albashin wasu daga cikin mambobinta da suka ki karbar sabon tsarin biyan albashi na bai daya wato IPPIS da gwamnatin tarayya ta kawo domin dukkan ma’aikatan gwamnati.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel