Magance matsalar tsaro: Buhari ya bada umurnin yin garambawul a rundunonin tsaro

Magance matsalar tsaro: Buhari ya bada umurnin yin garambawul a rundunonin tsaro

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayar da umurnin yin garambawul a dukkanin bangarorin tsaro na kasar. Mai bashi shawara kan tsaro na kasa Babagana Monguno ya bayyana hakan bayan fitowa daga taron majalisar tsaro a fadar shugaban kasa, Abuja.

Mr. Monguno aranar Talata bayan fitowa daga taron majalisar tsaro ta kasa, ya ce shugaba Buhari ya bada umurnin yin garambawul a bangarorin tsaro na Nigeria.

A yayin yiwa 'yan jarida karin haske, Mr Munguno ya bukaci zaman lafiya, yana mai daukar alkawarin cewa shugaban kasa da hafsoshin tsaro zasu kawo karshen ta'addanci a Arewa.

Ya ce bayan tattauna batutuwan da suka shafi tsaron kasar a wajen taron, an kuma tattauna batu kan safara da tu'ammali da miyagun kwayoyi.

A cewarsa, Nigeria ta tashi daga cibiyar hada hada, zuwa cibiyar sarrafa magungunan da ake safararsu, wanda babbar matsala ce.

Ya yi nuni da cewa a kwanakin baya an rufe gine ginen sarrafa magunguna guda 17 a fadin kasar tare da yin kira da a hada hannu wajen kawo karshen fatauci da shan miyagun kwayoyi.

Har ila yau a wajen taron, shuwagabannin rundunonin tsaro sun yiwa Buhari bayani kan hanyoyin da suke ganin ya kamata abi don kawo karshen ta'addanci a kasar.

KARANTA WANNAN: Ganduje ya amince a bude cibiyoyin jarabawar JAMB masarautu 5 na Kano

Mai baiwa shugaban kasar shawara ya kuma yi tsokaci kan harin da aka kaiwa gwamnan jihar Borno Babagana Zulum da tawagarsa.

Magance matsalar tsaro: Buhari ya bada umurnin yin garambawul a rundunonin tsaro
Magance matsalar tsaro: Buhari ya bada umurnin yin garambawul a rundunonin tsaro
Asali: Twitter

Mr. Monguno, ya bayyana takaicinsa kan lamarin, yana mai cewa gwamna Zulum zai halarci taron ta yanar gizo kuma yayi bayani kan yadda lamarin ya faru.

A dangane da kashe kashe a Kudancin Kaduna, Monguno ya ce siyace kawai, kuma gwamnan jihar na yin iya bakin kokarinsa don kawo karshen lamarin.

Taron ya samu halartar mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa, Farfesa Ibrahim Gambari, sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha.

Sauran sun hada da Manjo Janar Babagana Monguno (mai ritaya), shuwagabannin tsaro bisa jagorancin shugaban rundunar tsaro na kasa, Janar Gabriel Olonisakin.

Shugaban rundunar sojin kasa, Laftanal Janar Tukur Buratai, da na sojin ruwa, V.A Ibok Ekwe Ibas, da na sojin sama, A.M Sadique Abubakar.

Daga cikin mahalarta taron akwai Sifeta Janar na 'yan sanda, IGP Mohammed Adamu, shugaban hukumar tsaro ta DSS, Yusuf Bichi, shugaban hukumar tsaro ta NIA, Ahmed Rufai.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel