Hukumar WAEC ta fitar da jadawalin jarrabawar 2020

Hukumar WAEC ta fitar da jadawalin jarrabawar 2020

Hukumar shirya jarabawar kammala karantun sakandire ta Yammacin Afrika WAEC, ta fidda jadawalin jarabawar shekarar 2020.

Gwamnatin Tarayya ta sanar da cewa, za a fara gudanar da jarrabawa ne tun daga ranar 17 ga watan Agusta har zuwa 12 ga watan Satumban 2020.

Cikin wata sanarwa da kakakin hukumar WAEC reshen Najeriya Demianus Ojijeogu ya sanya wa hannu a ranar Talata, ya shawarci dalibai su yi watsi da duk wasu jadawalai da suka rika yawo a baya.

A baya Legit.ng ta ruwaito cewa, Babban jami'in hukumar WAEC a Najeriya, Mista Patrick Areghan, bayyana a wani taron manema labarai da ya gudanar a Abuja ya sanar da cewa za a gudanar da jarrabawar cikin makonni biyar.

Hukumar WAEC ta fitar da jadawalin jarrabawar 2020
Hukumar WAEC ta fitar da jadawalin jarrabawar 2020
Asali: UGC

Ya tunatar da manema labarai yadda annobar korona ta wajabta dage jarabawa wadda a baya aka kudiri gudanar da ita a tsakanin ranar 6 ga watan Afrilu zuwa 5 ga watan Yuni.

Ya ce a halin yanzu bayan bita kan halin da ake ciki, za a gudanar da jarabawar cikin tsawon lokacin da bai wuce makonni biyar ba, daga ranar 17 ga watan Agusta zuwa 12 ga watan Satumba.

Mista Patrick ya ce za rika gudanar da jarrabawar tun daga ranar Litinin har zuwa Asabar domin samun damar kammala ta cikin makonni biyar.

KARANTA KUMA: Buɗe Makarantu: NUC ta fara tantance jami'o'in Najeriya

Ya ce dalibai 1,549,463 ne suka yi rajistar zana jarrabawar a bana daga makaranrun 19,129, inda 786,421 suka kasance maza yayin da kuma 763,042 suka kasance mata.

Ya gargadi dukkanin makarantu da dalibai da su guji duk wasu ababe na satar jarabawa tare da cewa rashin aiwatar da kyakkyawan shiri ba zai taba zama uzuri na yi saba wa doka ba.

A karshe ya sanar da cewa, an aike da jadawalin karshe na jarabawar bana ga ofisoshin hukumar na yakuna da rassa daban-daban da kuma ma'aikatun ilimi na gwamnatin tarayya da kuma na jihohi.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel