Shuwagabannin tsaro basu da wa'adin ajiye mulki, Buhari ne kawai zai iya tsige su

Shuwagabannin tsaro basu da wa'adin ajiye mulki, Buhari ne kawai zai iya tsige su

- Lt. Gen. Alani Akinrinade (mai ritaya), ya ce shugaban kasa Muhammadu Buhari ne mai ikon sauke shuwagabannin tsaro

- Ya ce, shugaban tsaro na iya ajiye aiki, amma idan ka kai wancan matsayin to kana yiwa shugaban kasa aiki ne

- Akinrinade, ya ce dokar aikin gwamnati da ta ce masu shekaru 35 a aikin su yi ritaya, ya kawo nakasu sosai ga bangaren tsaro

Tsohon shugaban rundunar sojin kasa, Lt. Gen. Alani Akinrinade (mai ritaya), ya ce shugaban kasa Muhammadu Buhari ne mai ikon sauke shuwagabannin tsaro.

Shugaban kasa shine babban shugaban rundunonin tsaro na kasar, da suka hada da rundunar sojin sama, kasa da na ruwa, har ma da rundunar 'yan sanda.

Tsohon shugaban tsaron ya ce shuwagabannin tsaron za su iya yin murabus a kashin kansu idan har suka yarda da gazawarsu, ko kuma su jira shugaban kasa ya tsige su.

Akinrinade ya bayyana hakan a wata tattaunawa da manema labarai.

A baya bayan nan an samu yawaitar kiraye kiraye akan a tsige shuwagabannin tsaron saboda tabarbarewar tsaro a kasar, a makon da ya gabata majalisar dattijai ta bukaci Buhari ya tsige su.

Da aka tambaye shi ko yana goyon bayan a sauke shuwagabannin tsaron, Akinrinade ya ce shugaban kasa na da karfin ikon tsige su ko kuma ya ci gaba da aiki da su.

Ya ce, "Shugaban tsaro na iya ajiye aiki, amma batun tsigewa yana hannun shugaban kasa. Idan ka kai wancan matsayin to kana yiwa shugaban kasa aiki ne.

"Idan baya bukatar ka, to dole ka tafi. Idan kuma ka gamsu baka tabuka komai, ko ka gaji da aikin, sai ka tuntube shi ka sanar da shi. Ko ka rubutawa minista, wanda zai sanar da shugaban kasar.

KARANTA WANNAN: Dalilin da yasa Gemade da su Dogara suka koma APC - Mr Yekini Nabena

Shuwagabannin tsaro basu da wa'adin ajiye mulki, Buhari ne kawai zai iya tsige su
Shuwagabannin tsaro basu da wa'adin ajiye mulki, Buhari ne kawai zai iya tsige su
Asali: Twitter

"Idan baka da muradin barin aikin, sai ka jira umurnin ritaya daga shugaban kasa. Babu wa'adin ajiye aiki, matsalar kenan.

"Babu inda aka rubuta a dokar kasa cewa za ka rike mukamin shugaban tsaro na rundunar soji na tsawon shekaru hudu, ko shugaban tsaro na kasa na tsawon shekaru biyu. Babu wa'adi."

Akinrinade, ya ce dokar aikin gwamnati da ta ce masu shekaru 35 a aikin su yi ritaya, ya kawo nakasu sosai ga bangaren tsaro, saboda akwai bukatar jami'an tsaro masu yawa.

Ya bayyana cewa wasu zasu shiga aikin soji a shekarun kuruciya, amma dole su bar aikin da zaran sun kai shekaru 35 suna aikin.

Ya ce, "Ni bana tunanin wannan dabara ce saboda wanda ya cika shekaru 35 yana aikin gwamnati amma shekarunsa 56 a duniya, sai ace ya haura shekarun yiwa kasa hidima?

"Idan har mutumin yana aikinsa yadda ya kamata, sai ace mu kori irin wannan mutumin saboda ya yi shekaru 35 yana aiki?

"Wadannan wasu matsaloli ne da ke addabar kasar, da suke bukatar a sake yin duban tsanaki akansu."

Da aka tambaye shi kan kawo karshen matsalolin tsaro a kasar, Akinrinade ya ce zai zama abu mai wahala ya bada wannan shawarar ba tare da sanin hakikanin abunda ke faruwa a bangaren rundunar soji da kuma sanin manufar 'yan ta'addan kasar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng