WAEC: Za a buɗe duk makarantun tarayya 104 a ranar Talata - Nwajiuba

WAEC: Za a buɗe duk makarantun tarayya 104 a ranar Talata - Nwajiuba

A gobe Talata za a buɗe duk makarantun sakandire na gwamnatin tarayya 104 kamar yadda karamin ministan ilimi, Chukwuemeka Nwajiuba ya ba da sanarwa.

Ministan ya ba da sanarwar hakan ne a ranar Litinin, 3 ga watan Agusta, yayin da ya kammala tattaunawa da kwamishinonin ilimi na jihohi 36 da ke fadin tarayya da kuma sauran masu ruwa da tsaki.

Cikin sanarwar da mai magana da yawun ma'aikatar ilimi ta tarayya, Ben Goong ya sanya wa hannu, ya yabi shugabannin makarantun dangane da tabbatar duk wani shiri na komawar ɗalibai a gobe Talata.

Tun a ranar 26 ga watan Maris ne Gwamnatin Tarayya ta rufe duk makarantun kasa, matakin da ya shafi makarantun gwamnati da na masu zaman kansu.

Karamin ministan ilimi, Chukwuemeka Nwajiuba
Karamin ministan ilimi, Chukwuemeka Nwajiuba
Asali: UGC

A farkon watan Yuli ne gwamnati ta ce ɗaliban sakandare 'ya ajin ƙarshe za su koma ajujuwansu amma ba lallai ne hakan ta tabbata ba kasancewar gwamnatin ta ce ba za a rubuta jarrabawar WAEC ba ta 2020.

Sai dai a yanzu gwamnatin ta ba da umarnin a buɗe makarantu a gobe Talata domin 'yan ajin karshe na makarantun sakandire su kammala shirinsu na zana jarrabawar WAEC wadda za a fara gudanarwa a ranar 17 ga watan Agusta.

A yayin da karamin ministan ilimin ke sanar da ranar buɗe makarantun, ya kuma bayyana karara cewa sai an kiyaye ka'idodin dakile yaduwar cutar korona yayin komawa.

A cewarsa, dole ne kowace makaranta ta tanadi ruwan wanke hannu da kuma sunadarin tsaftace hannu (sanitizer).

Legit.ng ta ruwaito cewa, Jihohi Najeriya sun rarrabu dangane da damar da gwamnatin Tarayya ta bai wa ɗaliban ajin karshe ta komawa makarantu domin karasa shirin zana jarrabawar kammala karatun sakandire.

KARANTA KUMA: Mayakan IS sun dira kurkukun Afghanistan, sun saki daruruwan fursunoni

Binciken da jaridar The Punch ta gudanar ya nuna cewa, ɗaliban aji shida a jihohin Legas, Benuwe, Kwara da Ogun, na shirye-shiryen komawa a ranar Talata yayin da na jihar Cross River sun koma a yau Litinin.

Har yanzu jihar Enugu, Gombe, da Ribas basu sanar da ranar komawar ɗalibansu ba, sabanin jihar Ekiti inda ɗaliban za su koma a ranar 10 ga watan Agusta.

Haka kuma, gwamnatocin jihohi da dama sun gaza tanadar wuraren wanke hannaye a karkashin ruwa mai gudana da kuma sunadarin tsaftace hannu kamar yadda kwamitin shugaban kasa mai yaki da cutar korona ya shata.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel